Rundunar ’Yan Sandan jihar Kuros Riba ta tabbatar da kama malamin nan na tsangayar koyar da aikin shari’a a Jami’ar Kalaba, Farfesa Cyril Osim Ndifom, wanda ake zargi da yin lalata da dalibansa mata.
Rundunar ta ce an kama mutumin ne bayan an kutsa gidansa, sannan aka yi awon gaba da shi zuwa Babban Birnin Tarayya Abuja domin zurfafa bincike a kansa.
- Da takardun wani bakin Ba’amurike Tinubu yake amfani – Lauyan Atiku
- Yau sojojin Faransa za su fara ficewa daga Nijar
Hakan ya biyo bayan shafe sama da wata biyu da daliban tsangayar sun zarge shi da yi wa wasu daga cikinsu fyade, lamarin da ya jawo ce-ce-ku-ce.
Bugu da kari, hukumomin jami’ar sun sanar da dakatar da shi daga aiki har sai an gudanar da binciken a kan shi.
Amma da take yi wa Aminiya karin bayani, Kakakin rundunar a jihar, SP Irene Ugbo, ta ce an kama malamin ne a ranar Alhamis.
“Hakika jami’an tsaro da ba ’yan sanda ba sun kamashi sun tafi da shi,” in ji ta.
Zakaran malamin ya yi cara ne kan yi wa daliban tsangayar fyade, lamarin da ya jawo daliban suka yi zanga-zangar nuna bacin ransu a watan Agusta.
Wata majiya ta kusa da iyalan malamin ta shaida wa manema labarai da suka bi diddigin kama Ndifon cewa, “Da misalin karfe dayan dare ne muka ji wasu mutane masu yawa suna dukan kofar gidan suna cewa ku bude ko mu fasa kofar mu shigo. A haka dai suka shiga tafi da shi, amma ba mu san inda suka kai sh ba,” in ji majiyar.