Wata Kotun Majistare da ke zamanta a Ado-Ekiti a Jihar Eikiti, ta bayar da umarnin a tsare wani mutum mai shekara 42, Christopher Israel, a gidan gyaran hali bisa zargin yi wa ’yar cikinsa mai shekara 22 fyaɗe.
’Yan sanda sun tuhumi Israel da laifin yin fyaɗe da kuma cin zarafi.
- An kama ɗan wasan Manchester City kan zargin satar waya
- Ambaliya ta rushe gadar ta haɗa Arewa da yankin Kudu maso Yamma
Alƙalin kotun, Misis Olubunmi Bamidele, ba ta amsa roƙon Israel na yin shari’ar a sirrance.
Ta bayar da umarnin a ci gaba da tsare wanda ake zargin a gidan gyaran hali da ke Ado Ekiti, har zuwa lokacin da za ta nemi shawarar lauyoyi daga ofishin daraktan kararrakin jama’a.
Ta ɗage shari’ar har zuwa ranar 6 ga watan Nuwamba, 2024.
Tun da farko, mai gabatar da ƙara, Insifekta Olubu Apata, ya shaida wa kotun cewa Israel ya aikata laifin ne a ranar 21 ga watan Satumba a Ado-Ekiti.
Ya yi zargin cewa Israel ya yi wa ’yarsa mai shekara 22 fyaɗe, tare da ji mata rauni.
A cewarsa, laifin ya ci karo da tanadin sashe na 265 da na 256 na dokar laifuka ta Jihar Ekiti ta 2021.
Mai gabatar da ƙarar, ya buƙaci kotun da ta ci gaba da tsare Israel, har zuwa lokacin da ofishin DPP ya bayar da shawara kan shari’ar.