✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yau sojojin Faransa za su fara ficewa daga Nijar

Za a shafe wata uku kafin faransa ta kammala kwashe sojojin na ta gaba daga Nijar inda ake nuna wa juna yarda tsakaninsu da gwamnatin…

Faransa ta sanar cewa a yau ne sojojinta za su fara ficewa daga Jamhuriyar Nijar.

Za a shafe wata uku kafin Faransa ta kammala kwashe sojojin na ta gaba daga Nijar inda ake nuna wa juna yatsa tsakaninsu da gwamnatin sojin kasar da ta yi juyin mulki.

“A makon nan za mu fara kwashe sojojinmu cikin aminci da hadin kan jamhuriyar Nijar,” kamar yadda ta sanar.

Hakan na zuwa ne makok guda bayan Jakadan Faransa a Nijar ya bar kasar sakamakon matsin lamba daga gwamnatin sojin.

A ranara 24 ga Satumba Shugaba Emmanuel Macron ya sanar cewa kasarsa za ta kwashe sojojinta 1,400 “kafin karshen waan Disamba” daga Nijar.

Faransa at girke sojojinta a Nijar domin taimaka wa yaki da masu ikirarin jihadi da suka addabi yankin Sahel.

Gidan rediyon Faransa na RFI ya ruwaito cewa sojojin kasar 400 ne ke aiki tare da dakarun Nijar a garin Ouallam na kasar Nijar da ke iaka da kasashen Burkina Faso da Mali inda hare-haren kungiyar ISWAP suka yi kamari.

Tun bayan juyin mulkin da sojoji suka yi a Nijar suka fara neman dakarun Faransa su fice daga kasar shiga a yayin da al’ummar kasar suka gudanar da zanga-zangar neman Faransa ta fice daga kasar.

Korar da gwamnatin sojin da a yi juyi mulki a Mali ta yi wa dakarun Faransa a kasar ya sa suka koma Nijar, inda yanzu za su bari su kuma Jamhuriyar Nijar ko kuma Benin.