✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jami’an tsaro sun kai samame kan masu sayar da raguna a Legas

An kwashe dabbobi da dama waɗanda aka kai kasuwar Abbatuwa ta Legas don tantance lafiyarsu.

Kwamitin tsaro na haɗin kai da ya haɗa da ’yan sanda da sauran hukumomin tsaro da haɗin gwiwar Ma’aikatar Noma ta Jihar, ya kai samame a kan masu sayar da ƙananan dabobbi da suka haɗa da raguna, tumaki da awaki da ke kasa su a gefen titi, a birnin da sauran wuraren da gwamnati ba ta a amince da su ba.

Kwamitin tsaron na haɗaka a ƙarƙashin jagorancin Shugaban Hukumar, Babban Sufurtandan ’Yan sanda (CSP) Shola Jejeloye ya faro samamen ne daga ’yan raguna da ke Unguwar Mangwaro a Agege, inda jami’an suka kwashe dabbobi da dama waɗanda aka kai kasuwar Abbatuwa ta Legas don tantance lafiyarsu.

CSP Jejeloye ya bayyana wa manema labarai cewa dillalan dabbobin suna gudanar da harkokinsu cikin rashin tsafta wanda hakan ke janyo haɗari ga masu masu saye da sauran abokan hulɗarsu, da masu ababen hawa da ke kai-komo a titunan da masu dabobbin ke baza hajarsu.

CSP Jejeloye ya ce “Dagawannan wurin, a bayyane yake cewa dabbobin ba a tsare su yadda ya kamata ba, kuma cikin sauƙi rago zai iya kwancewa ya hau kan titin wanda zai iya haifar da haɗari.”

Ya shawarci masu harkar dabobbin a gefen hanya ko inda ba a yarda ba a faɗin jihar su yi biyayya da kuma tabbatar da cewa an yi wa dabbobinsu gwajin ƙoshin lafiya yadda ya kamata.

Ya buƙaci kuma su tabbatar suna cinikinsu ne a wuraren da hukuma ta amince kaɗai, inda yi gargaɗin cewa duk wanda aka kama yana jefa rayuwar ’yan Legas a cikin haɗari ta hanyar gudanar da sana’arsa ta hanyar son kai, to za a ƙwace dabbobinsa, su zama mallakin gwamnatin jihar.

Ya shawarci mazauna yankin da masu amfani da dabobbi su tabbatar sun sayi dabbobin daga hannun ’yan kasuwar da aka tabbatar da sahihancinsu, don guje wa abubuwan da za su iya haifar da matsala ga lafiyarsu.

Shugabar Sashen Sa-ido da Karɓar Ƙorafe-Ƙorafe na Ma’aikatar Muhalli ta Jihar Legas, Dokta Kofoworola Oloritun ta ce mutanen da ke sayar da dabbobi a gefen titi sun keta dokokin muhalli da noma na jihar ta hanyoyi da dama.

Ta ce kafin a baje kowace dabba don sayarwa, ya kamata a fara duba wannan dabbar domin tabbatar da ba ta da cuta.

Ta ƙara da cewa, “Mun yi gargaɗi ga waɗannan mutane a lokuta da dama, amma sun yi kunnen ƙashi, dabbobin da aka kwashe daga ’yan raguna da suke hada-hada ba bisa ƙa’ida ba, za a yi nazarinsu yadda ya kamata a nan gidan hikima na Abbatuwa kafin masu ruwada- tsaki su gana da masu su tare da faɗakar da su kan bin dokokin da aka gindaya dangane da sayar da dabbobin,” in ji ta.

Ta kuma bayyana cewa za a ɗora tarar da ta dace ga masu gudanar da kasuwancin dabobbin ba bisa ƙa’ida ba kafin a miƙa musu dabbobinsu.