✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jami’an tsaro sun daƙile harin Boko Haram sun kashe mayaƙa 5 a Borno

Warambe na daga cikin yankunan da mazanaunansu suka dawo da zama a baya-bayan nan, kuma mayaƙan Boko Haram sun sha yin yunƙurin kurɗawa cikinsa

Sojoji da mafarauta don halaka mayaƙan Boko Haram biyar tare da daƙile wani hari da ’yan ta’addan suka kai a ƙauyen Warambe da ke Ƙaramar Hukumar Gwoza a Jihar Borno.

Warambe na daga cikin yankunan da mazanaunansu suka dawo da zama a baya-bayan nan, kuma mayaƙan Boko Haram sun sha yin yunƙurin kurɗawa cikinsa.

Shugaban mafarautan wanda ɗan asalin garin ne ya ce a safiyar Juma’a ne maharan suka nemi shiga ƙauyen, “amma muka gana  su, muka kashe mutum biyar daga cikinsu. An miƙa makaman da muka ƙwato daga hannunsu ga sojoji.”

Sanata Mohammed Ali Ndume mai wakiltar Kudancin Borno, ya jinjina wa ƙoƙarin jami’an tsaron, musamman wajen ɗaukar mataki cikin gaggawa yana mai ba su ƙwarin gwiwar su ƙara jajircewa.

Sanata Ndume yace ce, “ina farin cikin sanar da ku cewa an kashe ’yan ta’adda biyar a ƙauyen Warambe. Ina kunjinjina wa mafarauta da kuma yadda aka yi saurin ɗaukar matakin tura sojojin rundunar ‘Operation Hadin Kai’ zuwa wurin, wanda ya ƙara wa al’ummar yankin ƙwarin gwiwa.”

Makaman da aka ƙwato sun hada da bindiga ƙirar AK47 guda biyu da harsasai, kuma an damƙa su a hannun sojoji.