Jami’an tsaro da suka hada ’yan sanda da sojoji sun kubutar da fasinjoji 76 a kan hanyar Funtua zuwa Zaria da ke Jihar Kaduna.
Bayanai sun ce jam’ian tsaron sun yi galaba a kan ’yan bindigar da suka yi kokarin yin garkuwa da mutanen daf da kauyen Gulbala da ke Karamar Hukumar Giwa ta jihar.
- Kaso 60 na ’yan Arewa ba su da asusun ajiya na banki – Uba Sani
- Girgizar kasa ta halaka kusan mutum 20 a Indonesia
- Ecuador ta lallasa Qatar a wasan farko na Gasar Kofin Duniya
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Mohammed Jalige, ya fitar a ranar Litinin.
Ya bayyana cewa lamarin ya faru ne a ranar 18 ga watan Nuwamba, 2022 da misalin karfe 11 na dare lokacin da hedikwatar rundunar ‘yan sanda, Giwa ta samu rahoton cewa ‘yan bindiga da dama dauke da muggan makamai sun tare hanya da nufin sace matafiya.
A cewarsa, nan take aka tura tawagar ‘yan sanda da sojoji domin tarwatsa ‘yan bindigar a hanyar.
DSP Jalige, ya ce an kai daukin gaggawa inda jami’an tsaron suka fattaki ‘yan fashin dajin, lamarin da ya sa suka yi watsi da wannan mummunan kudiri nasu suka arce.
“Binciken farko da aka gudanar ya nuna cewa wadanda abin ya rutsa da su da suke cikin motar sun taso ne daga Karamar Hukumar Sabon Birni ta Jihar Sakkwato da nufin zuwa wurare daban-daban, yayin da barayin suka tare su,” in ji shi.
DSP Jalige ya kuma ce jami’an tsaro na ci gaba da gudanar da bincike a yankin don nemo direban babbar mota da wasu fasinjoji biyu da har yanzu ba a kai ga tantance su ba.
Ya ce Kwamishinan ‘Yan sandan jihar, Yekini Ayoku ya bayyana cewa, an samu wannan nasara ce sakamakon hadin kai da suke ci gaba da samu a jihar.
Ya ba da tabbacin cewa za su ci gaba da hada kai da sauran jami’an tsaro don kakkabe masu aikata miyagun laifuka.