Rundunar tsaro ta ‘Operation Thunder Strike’ ta ceto mata biyu da aka yi garkuwa da su a Gadanin Gwari dake yankin Gwagwada a karamar hukumar Chikun ta jihar Kaduna.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Kwamishinan Tsaro da Al’amuran Cikin Gida na jihar, Samuel Aruwan ya fitar ranar Asabar.
- Sojoji mata 200 za su yi sintiri a hanyar Abuja-Kaduna
- Gwamnatin Kaduna ta sanar da ranar sake bude makarantun sakandiren jihar
- ’Yan bindiga sun hallaka mai juna biyu a hanyar Kaduna
- Mutum 6 sun mutu a harin ’yan bindiga a Kaduna
A cewar sanarwar, “Sojoji sun yi nasarar yin artabu da ‘yan bindiga har suka ci karfinsu, wasu kuma suka gudu.
“Uku daga cikin ‘yan bindigar sun shiga hannu, an tseratar da mata biyu da suka yi garkuwa da su,” cewar Aruwan.
Kwamishinan ya kuma ce ‘yan bindigar sun yi garkuwa da matan ne yayin da suke kan hanyarsu ta zuwa gona.
Kazalika, ‘yan sandan jihar Kaduna sun ceto mutane biyu da aka yi garkuwa da su a yankin Kurmin Idon, dake kan titin Kaduna zuwa Kachia a karamar hukumar Kajuru.
Aruwan ya kara da cewa tuni rundunar tsaron ta ci gaba sintiri a babbar hanyar Kaduna zuwa Abuja.
Kwamishinan ya kara da cewa gwamnan jihar, Mallam Nasir El-Rufai, ya jinjinawa sojojin da ‘yan sandan jihar kan yadda suka ceto mutanen da aka yi garkuwar da su.