✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jami’an tsaro sun ceto manoma 36 daga hannun ’yan bindiga a Kebbi

Tawagar haɗin gwiwa ta ’yan sanda, sojoji da ’yan sa-kai, sun ceto manoma 36 da ’yan bindiga suka sace a kan hanyar Mairairai/Bena da ke…

Tawagar haɗin gwiwa ta ’yan sanda, sojoji da ’yan sa-kai, sun ceto manoma 36 da ’yan bindiga suka sace a kan hanyar Mairairai/Bena da ke Ƙaramar Hukumar Danko/Wasagu a Jihar Kebbi.

Kakakin rundunar ’yan sandan jihar, SP Nafiu Abubakar, ya bayyana cewa ’yan bindiga sun tare manoman da ke dawowa daga gonakinsu, inda suka yi awon gaba da su.

Rundunar haɗin gwiwar ta yi gaggawar kai ɗauki, inda suka fafata da ’yan bindigar.

Daga bisani, jami’an tsaro sun yi nasarar fatattakar ’yan bindigar zuwa cikin daji, yayin da wasu daga cikinsu suka tsere da raunukan harbin bindiga.

Sanarwar ta tabbatar da cewa an ceto dukkanin manoma 36 ba tare da sun samu rauni ba, kuma an miƙa su ga iyalansu.

Kwamishinan ’yan sandan jihar, Bello M. Sani, ya yaba wa jami’an tsaron bisa jarumtar da suka nuna tare da ƙwarewa.

Ya kuma buƙace su da su ci gaba da jajircewa wajen tabbatar da tsaro a jihar.

Haka kuma ya yi kira ga dukkanin hukumomin tsaro a yankin da su ƙara haɗa kai don yaƙi da ’yan bindiga da sauran masu aikata miyagun laifuka.