✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jami’an tsaro na izgili ga mutanen da aka kai wa hari —Sarkin Musulmi

Sarkin Musulmi ya ce a ’yan kwanakin nan, jami’an tsaro sun zama masu yin izgili ga al'ummomin da 'yan bindiga suka kai wa hari.

Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Muhammadu Sa’ad Abubakar III, ya ce a ’yan kwanakin nan, jami’an tsaro sun zama masu yin izgili ga al’ummomin da ‘yan bindiga suka kai wa hari.

Sarkin Musulmin wanda tsohon soja ne, ya ce a ‘yan kwanakin nan, jami’an tsaro na zuwa wuraren da ‘yan ta’dda suka kai hari ne domin yi wa mutanen yankunan izgili, bayan an kai hari.

Ya yi wannan furuci ne a taron Kungiyar Addinai ta Najeriya (NIREC) karo na biyu na 2023, a Abuja, inda ya nuna damuwa kan sake tabarbarewar rashin tsaro bayan zaben 2023.

Ya ce, “A lokacin yakin neman zabe da ma zaben babu wadannan matsalolin na rashin tsaro, amma kwatsam bayan zabe sai kashe-kashe suka dawo a jihohin Neja da Kaduna da Filato da sauransu.

“Laifin wasu jami’an tsaro ne da sai bayan ’yan ta’adda sun kai hari, su kashe mutane, su lalata musu dukiyoyi, ba tare da wata turjiya ba.

“Sai daga bisani jami’an tsaro su zo, watakila don yi wa jama’a izgili ko ba’a ko kuma su kalli tokar abubuwan da aka lalata.

“Amma tunda sabuwar gwamnati za ta shigo, za mu iya sa ta taka rawar gani wajen magance wadannan matsalolin.

“Amma ba za mu iya ci gaba a haka ba, domin idan har ‘yan bindiga za su iya shiga cikin jama’a, su kashe su su kona gidaje, amma sai daga baya jami’an tsaro za su je wurin, to babu amfani.”