✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Jami’an tsaro na aiki tare da ’yan bindiga —Gumi

Malamin ya ce akwai rashin adalci idan aka kwatanta IPOB da ’yan bindiga.

Fitaccen malamin addinin musulunci a Najeriya, Sheikh Ahmad Gumi, ya ce wasu daga cikin jami’an tsaro na hada kai da ’yan bindiga wajen yin barna a fadin kasar.

Gumi ya yi wannan kalamai ne yayin wata hira da gidan talabijin na Arise ya yi da shi a ranar Laraba.

  1. Karin kasafin N895bn: Majalisa ta kammala karatun farko
  2. Farouk Lawan: Ba za a iya gurfanar da wanda ya ba da rashawar ba

“An kama su a Zamfara; an kama su a ko ina, ta yaya wadannan makaman suke ketare iyakokin kasar nan?

“Dole daga cikin bata garin jami’an tsaro akwai wanda suke ba wa ’yan bindiga hadin kai har makaman suke samun shiga dazuka.

“Ba zai taba yiwuwa bai dan na bada irin makaman na ce ka shiga da su daular turawa, saboda a can ana saka ido sosai kan harkar tsaro.

“Idan baka sani ba wadannan ’yan bindigar na aiki tare da bata-garin jami’an tsaro.

Wasu na kasuwanci da wannan harka, kuma mutane da dama na da hannu a ciki, za a yi mamaki idan ka ji ko su wa ke taimaka musu, in ji Gumi.

Gumi, ya bayyana cewar ta’addancin ’yan bindiga ya zama hanyar samun kudi ga wasu, yana mai cewa babu yadda za a yi ’yan bindiga su rika mallakar makamai ba tare da hadin kan jami’an tsaro ba.

“Idan ana son yakar ’yan bindiga sai an sauya wani bangaren na sha’anin tsaron kasar nan.”

Kazalika malamin ya ce rashin adalci ne idan aka kwatanta ’yan bindiga da masu fafutikar kafa kasar Biyara (IPOB).

“IPOB suna kashe ’yan sanda da sojoji sannan suna kone ofisoshin Hukumar Zabe (INEC), gine-ginen gwamnati; da kashe mutanen da basu ji basu gani ba.

“’Yan bindiga suna sace yara ne don su samu kudi ba wai su kashe su ba; don haka ba zaka hada su da wanda suke kashe jami’an tsaro da wanda yake satar yara don ya samu kudi ba. Yana da kyau muke yin adalci a al’amuranmu,” a cewarsa.