Jami’an tsaro a Jamhuriyyar Nijar sun kama wadansu mafarauta uku ’yan Najeriya da ake zargi da satar damun daji, a daya daga cikin gandun dajin duniya da ke yammacin Afirka.
Mafarautan ’yan Najeriya, an kama su ne a Kudu maso Yammacin garin Dosso a cikin motar daukar kaya biyu da ke cike da hauren giwa da fatun maciji da kan wasu namun dawa da dama da suka kunshi bauna da birai, kamar yadda Kamfanin Dillacin Labarai na AFP ya ruwaito.
Ana zargin cewa mutanen sun yi farautar namun dajin ne daga wani babban gandun daji da ya hada kan iyakar Nijar da Burkina Faso da Jamhuriyyar Benin.
Gwamnatin Nijar ta ce ta kuma kama bindigogin farauta da dama da wasu sinadarai da mafarautan ke dauke da su.
Gandun dajin na kasa-da-kasa, mallakin Majalisar Dinkin Duniya ne kuma yana da girma sosai, wanda kuma ke kunshe damun daji da dama.