Jami’ar Yusuf Maitama Sule da ke Kano (YUMSUK) ta sanar da dakatar da rubuta jarrabawar da dalibanta suke yi saboda yajin aikin da direbobin Adaidaita Sahu suka fara yi a Jihar.
A ranar Litinin ne dai direbobin babur din mai kafa uku, wanda aka fi sani da Adaidaita Sahu a Jihar suka shiga yajin aikin, saboda wata rashin fahimta tsakaninsu da Hukumar da ke Kula da Ababen Hawa ta Jihar (KAROTA), kan sabunta lasisin tuki.
- Kotu ta umarci a saki zakaran kwallon tennis na duniya, Novak Djokovic
- Sai Buhari ya bar mulki za a ga amfaninsa — Bashir Ahmad
A cikin wata wasika da jami’ar ta rarraba wa dukkan sassanta ranar Litinin, wacce Aminiya ta gani, jami’ar ta kuma ba da umarnin fito da manyan motocinta domin jigilar dalibai zuwa wasu muhimman wurare.
A cewar sanarwar, “Dukkan jarabawar da aka tsara yi ranar Litinin, 10 ga watan Janairun, yanzu an dageta.
“Dukkan wacce kuma aka tsara yinta tsakanin karfe takwas zuwa 11 na ranar Talata, su ma an dage su.
“Amma dukkan wadanda aka tsara yi daga 11:30-2:30 da kuma na 3:00-6:00 l, za su gudana kamar yadda aka tsara.
“Jami’ar ta kuma amince a fito da motocinta na bas-bas domin jigilar dalibai zuwa muhimman wurare saboda a rage musu radadin rashin hanyoyin sufurin.
“Dukkan jarrabawar da aka soke za a sake sanar da rana da lokacin yinta a nan gaba,” inji sanarwar.
Baburan Adaidaita Sahu dai su ne kaso mafi yawa na hanyoyin sufuri a birnin Kano.
Yajin aikin dai ya tilasta wa mutane da dama tafiya a kasa, wasu kuma suka koma amfani da motocin daukar kaya wajen sufuri.