A yau Litinin 15 ga watan Junairu ne za a fara rajistar jarabawar shiga makarantun gaba da sakandare (UTME) ta shekarar 2024.
Hukumar Jarabawar Shiga Makarantun Gaba da Sakandare (JAMB) ta bukaci dalibai kada su biya masu cibiyoyin rajistar jarabawar (CBT Center) ko sisi, saboda a cikin kudin fon dinsu har da na rajista a ‘CBT Centre’.
Jami’in Hulda da Jama’a na hukumar, Fabian Benjamin ya sanar cewa “JAMB ce za ta tattara duk kudaden sannan sannan daga bisani ta biya CBT Center rabonsu.
“Kamar yadda aka yi bara, zuwa kawai dalibi zai yi cibiyar CBT a yi masa rajista ba tare da ya biya su ko sisi ba.”
- NAJERIYA A YAU: Mece Ce Makomar Jam’iyyar APC A Jihar Kano?
- Pantami ya samo N50m daga kudin fansan ’yan uwan Nabeeha
JAMB ta ba da lissafin kudaden da za biya da suka ha da da N3,500 na fom din UTME/DE, kudin CBT N700, da kudin MOCK/UTME N500. Jimillar kudin dalibin da ba zai yi mock din ba N6,200, na wanda zai zana mock kuma N7,700.
Sanarwar ta ce, tsarin rajistar UMTE da DE za su ci gaba da kasancewa ba tare da biyan kudi kai-tsaye ba, domin kare dalibai daga fadawa hannun ’yan damfara a cibiyoyin CBT.
Hukumar ta kuma sanya ranar 7 ga Maris, 2024, don jarabawar gwaji (Mock-UTME), yayin da na ainihin kuma zai zai gudana daga 19 zuwa 29 ga Afrilu, 2024.
Hakazalika za a fara sayar da fom din neman gurbin shiga manyan makarantu kai tsaye (DE) d akuma E-pin ranar Laraba 28 ga Fabrairu, a rufe Alhamis 28 ga Maris 2024.
Jami’in Hulda da Jama’a na JAMB, Fabian Benjamin ya ce masu rubuta jarabawar za su buga fom din jarrabawarsu daga ranar 10 ga Afrilu, 2024.