✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

JAMB: Talata sakamakon jarabawar 2023 zai fito

Ranar Asabar JAMB za ta sake Jarabawar daliban da suka samu matsala

Hukumar Shirya Jarabawar Shiga Manyan Makarantu (JAMB) ta ce a ranar Talata za ta fitar da sakamakon jarabwarta ta 2023.

Hukumar ta bayyana cewa a ranar Asabar, 6 ga watan Mayu da muke ciki kuma, za ta gudanar da jarabawa ga daliban da suka samu matsala a jarabawar farko.

Kakakin JAMB Fabian Benjamin ya sanar cewa hukumar ta jinkirta sakin sakamakon jarabawar zuwa ranar Talata ne domin tabbatar da cika ka’idoji da sahihanci da kuma magance matsaloli.

Ya bayyana cewa, “Dalibai za su duba sakamakon jarabawarsu ranar Talata 2 ga Mayu, 2023, wadanda suka samu matsala kuma ba za su ga nasu ba, sai dai su samu sakon ranar da za a sake jarabawar.”

Jami’in ya kara da cewa wadanda ba su samu rubuta jarabawar ba, saboda dalilan da ba su suka jawo ba ne za su maimaita jarabawar a ranar 6 ga watan Mayu.

Daliban sun hada da wadanda aka tantance amma ba su samu rubuta jarabawa ba da wadanda aka samu bambanci a bayanansu sai kuma wadanda na’ura ta kasa tantancewa.

Benjamin ya bukaci daliban da hakan ta shafa da su sake buga katinsu na jarabawa daga ranar 4 zuwa 5 ga watan Mayu, domin sanin wuri da kuma lokacin jarabawarsu.

Ya ce daga cikin dalibai miliya 1.59 da suka rubuta jarabawar, mutum dubu 80 sun nuna bajinta.