✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Jama’ar gari sun kona masu kwacen waya da ransu

Bayan sun yi wa wata mata kwacen waya a bainar jama'a ne mutane suka yi musu kofar rago

Jama’ar gari sun cinna wa wasu masu kwacen waya wuta da ransu bayan da bata-garin suka kwace wa wata mata waya da jakar hannu rana tsaka.

Wani ganau ya shaida wa wakilinmu cewa mutanen su uku sun zo ne a cikin babur mai kafa uku suka kwace wa matar waya da jakar hannu a bainar jama’a a garin Anaca, Jihar Anambra.

“A nan suka tsaya suka yi wa matar kwacen waya da jakar hannunta, sannan suka koma suka shiga babur dinsu za su wuce, amma babur din ya ki tashi.

“A lokacin ne wasu matasa da ke lodin motoci a tashar mota da sauran mutane suka yi musu kofar rago, suka fara jibgar su.

“Ana cikin dukan nasu ne wasu suka je suka zo da tayoyi, wasu suka kawo man fetur aka bulbula musu, aka cinna musu wuta da ransu.”

Shaidan gani da idon ya bayyana cewa daya daga cikin masu kwacen wayan ya samu ya tsere a lokacin da jama’a ke kokarin kama su a fara yi musu bugun kawo wuka.

Jami’in Hulda da Jama’a na Rundunar ’Yan Sandan Jihar Anambra, Tochukwu Ikenga, ya tabbatar wa wakilimu cewa an cinna wa mutum biyun wuta da ransu, amma na ukun ya tsere.

Ya ce, ’yan sandan da aka tura bayan faruwar lamarin sun kwantar da kurar da ta tashi, sannan an mayar wa matar wayarta da jakarta, babur din masu kwacen wayan kuma yana hannun hukuma.

Tochukwu ya bayyana cewa ’yan sanda na ci gaba da aiki domin cafko mutum na ukun da ya tsere a cikin masu kwacen wayan.