’Yan bindiga 21 sun sheka lahira bayan jama’ar gari da ’yan banga sun yi musu kwanton ɓauna a yankin Danko Wasagu na Jiajr Kebbi.
Shugaban Ƙaramar Hukumar Danko Wasagu, Hussaini Aliyu-Bena, ya ce ’yan bindigar na tsallakowa zuwa Jihar Kebbi daga yankin Mariga na Jihar Neja ne, ’yan banga da jami’an tsaro suka yi musu kwanton ɓauna a Tudun Bichi suka kashe 21 daga cikinsu.
- ’Yan sanda sun cafke ’yan bindiga ɗauke da makamin roka a Yobe
- An tono gawar mawaki Mohbad don binciken musabbabin mutuwarsa
Ya bayyana cewa ƙaramar hukumarsa ta yi iyaka da yankin Mariga, shi ya sa ’yan ta’addan suke samun sauƙin tsallakowa zuwa Jihar Kebbi ta nan.
Ya ce ’yan bindiga sun kashe Marafan Mai Inuwa da ke yankin Kanya, suka yi garkuwa da wasu mutane, amma daga baya sojoji sun ƙwato mutanen.
Ya roƙi gwamnati ta girke ƙarin sojoji a yankunan Malekachi da Dankade, inda ’yan bindiga suke bi su wuce.
Sannan ya yaba da ƙoƙarin jami’an tsaro da ’yan banga da sauran mazauna yankin wajen daƙile ayyukan ’yan bindiga.
Shugaban Karamar Hukumar ya ce Gwamna Nasiru Idris ya ba da umarni a ziyarci al’ummar ƙauyukan da suka yi gudun hijira zuwa yankin Kanya a jajanta musu.
Aminiya ta nemi samun ƙarin bayani daga kakakin ’yan sandan jihar, SP Nafiu Abubakar, amma ya shaida wa wakilinmu cewa bai samu rahoto ba tukuna.