✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Jama’ar gari sun kashe ’yan bindiga 4 a Neja

’Yan bindigar sun kashe mutum 15 a harin ramuwar gayya.

’Yan bindiga akalla hudu ne suka sheka lahira bayan ’yan banga da mafarauta sun ritsa su, sun ragargaje su a kauyen Magami da ke Karamar Hukumar Shiroro ta Jihar Neja.

’Yan bindigar sun kai harin ne a ranar Alhamis, amma suka gamu da gamonsu a hannun ’yan bangar.

A ranar Juma’a kuma ’yan bindigar suka kai wa mutanen kauyen harin ramuwar gayya inda suka hallaka akalla mutum 15, wasu da dama kuma ba a san inda suke ba.

Majiyarmu a Shiroro, ta ce “da suka lura cewa mafarautan da ’yan banga sun koma sansaninsu da ke Galadima Kogo, sai maharan suka dawo suna gadara gami da harbin duk wanda suka gani.

“Abin taikaici, sun yi amfani da muggan makamai ne wajen kashe mutanen da ba sa dauke da makami”.

Majiyar ta tabbatar da mutuwar mutum shida da Unguwar Magiro a Karamar Hukumar Rafi, sai kuma mutum hudu a Farin Hula da wasu  biyar a Magami a Karamar Hukumar Shiroro.

Ta kara da cewa wasu mutane da dama kuma ba a gan su ba, a yayin da wasu ke gudun hijira zuwa garin Kuta, hedikwatar Karamar Hukumar Shiroro, domin tsira da rayukansu.

A zantawarta da wakilinmu, Kungiyar Matasa Masu Kishin Karamar Hukumar Shiroro ta yi kira ga gwamnati ta da tura jami’an tsaro da ’yan banga da mafarauta su samar da tsaro a yankin domin al’umma su koma su ci gaba da gudanar da harkokinsu yadda ya kamata.