✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jama’a sun kashe ‘barawon babur’, sun kone gawarsa a Gombe

Jama’a sun kashe ‘barawon babur’, sun kone gawarsa a Gombe

Wasu fusatattun mutane sun kashe wani da ake zargin barawon babur ne kuma sun bankawa gawarsa wuta a kusa da babbar kasuwar garin Gombe.

Ana zargin mutumin ne da sace babur ne da wani kwastoman banki ya ajiye a gaban bankin Ja’iz, ya shiga don karbar kudi, inda fusatattun mutanen suka cinna masa wuta.

Wani da lamarin ya faru akan idonsa da ya nemi a sakaya sunansa, ya ce barawon ya nemi ya tsere da babur din.

Sai dai a lokacin da mai babur din ya fito ya yi ihun barawo inda nan take ’yan acaba suka bi shi aka kama shi.

Ya ce jama’a cikin fushi suka dinga dukansa suna buga masa dutse kafin daga bisani suka kashe shi suka cinna wa gawar wuta.

Ya Kara da cewa bayan an Kona Barawon jami’an Yan sanda sun zo wajen sun tattara gawar suka tafi da ita.

“Sai mai babur din da ya yi sauri ya bar wajen domin yana tsoron tambayoyin da zai fuskanta daga jami’an ’yan sanda a lokacin bincikensu,” in ji shi.

Da yake tabbatar da lamarin, jami’in hulda da jama’a na Rundunar ’Yan Sandan Jihar, ASP Mahid Mu’azu Abubakar, cewa ya yi tuni wanda ake zargin aka tafi da gangar jikinsa zuwa asibiti don tabbatar da mutuwar sa ko akasin haka.

Ya ce jami’an su sun isa wajen da lamarin ya faru cikin gaggawa inda suka tattara gangar jikin zuwa asibiti.

Sai dai duk da kona barawon, Kakakin ’yan sandan ya ce lilkitoci ne kawai za su iya tabbatar da mutuwarsa.

Daga nan sai ya yi kira ga jama’a da su guji daukar doka a hannunsu, inda ya ce hakan ba daidai ba ne.