Jama’ar gari sun fasa wani rumbun ajiyar hatsin gwamnati da ke Abuja, inda suka wawushe kayan abincin da ke ciki.
Da sanyin safiyar Lahadi ne bata-garin suka yi dirar mikiya suka balla rumbun ajiyar abincin da ke garin Gwagwa, suka fara awon gaba da hatsin ciki.
Mazauna yankin sun ce bata-garin sun isa rumbun abincin da ke yankin Tasha ne da misalin karfe 7 na safe, suna kinkimo buhunan abincin da ke dauke da tambarin Gwamnatin Tarayya.
Wani mazaunin unguwar Karmo da ke kusa da wurin mai suna Ja’afar Aminu ya ce an shafe sama da awa biyu ana kwasar kayan abinci daga dakin ajiyar.
- An sa kyautar N50m don samun bayani kan ’yan bindiga 2 a Katsina
- Mafitar Taƙaddamar Gwamnan Kano Da Shugaban Hisbah
A cewarsa, mazauna Karmo da makwabtansu daga yankin Jiwa suna tururuwar zuwa kwasar abincin, lamarin ya haifar da cinkoson ababen hawa a kan hanyar Gwagwa zuwa Karmo zuwa Jabi da Dei-Dei.
Ja’afar ya ce shi kansa yi kokarin zuwa wurin amma ya hakura, saboda raunukan da ya samu a yamutsin.
Wani mazaunin Karmo, Christopher Agbo, ya ce wasu daga cikin dandazon mutanen da suka yi wa wurin dirar mikiya suna rika yin awon gaba da karafunan da ke wurin da sauran kayan gwangwan.
Shi ma wani dan unguwar da ya ce ya hadu da mutane dauke da buhunan hatsin, Sani Yusuf, ya ce mutanen suna kokawa da cewa kayan abincin ba za su ciwu ba, domin sun riga sun rube.
Wasu daga cikin matasan sun nufi rukunin masana’antu na Idu da ke Abuja, inda kamfanoni ke da rumbunan ajiya, ciki har da wadanda gwamnati ta kama haya domin adana.
Sai dai wakilinmu ya tuntubi mai magana da yawun rundunar ’yan sandan Abuja, Josephine Adeh, wadda ta shaida masa cewa sun samu rahoton abin da ke faruwa kuma tun sun tura jami’ansu domin shawo kan lamarin.
Irin haka ta faru da kayan tallafin a lokacin annobar COVID-19 a Abuja, inda bata-gari suka far wa rumbuna ajiyar.