✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An sa kyautar N50m don samun bayani kan ’yan bindiga 2 a Katsina

’Yan sanda sun yi alkawarin tukwicin N50m ga duk wanda ya ba ta bayani har aka kamo wasu kasurguman ’yan bindiga 2 a Jihar Katsina

Rundunar ’yan sandan jihar Katsina ta yi alkawarin bayar da tukuicin Naira miliyan 50 ga duk wanda ya taimaka da bayanai da suka kai ga kama wasu gaggan ’yan bindiga biyu masu suna Modi Modi da kuma Jan Kare.

Sanarwa  da kakakin rundunar, Abubakar Aliyu, ya fitar ta ce yi zargin cewa Modi Modi da Jan Kare ne ke da alhakin yawancin hare-haren ta’addanci a jihar, musamman a yankunan kananan hukumomin Kankara da Safana.

“Tsaron mazauna yankin yana da matukar muhimmanci, shi ya sa muka dauki wannan mataki.

“Muna daukar kwararan matakai kan masu aikata laifuka da ke barazana ga zaman lafiya da kwanciyar hankalin al’umma,” in ji sanarwar.

Aliyu ya yi alkawarin cewa rundunar za ta tsare sirrin duk wadanda suka taimaka da ba bayanan da kuma kuma bayanan suka bayar.

“Ana kira ga al’umma da su ba taimaka mana da duk wani bayani da zai taimaka wa jami’an tsaro wajen kamo masu shirya garkuwa da mutane da ta‘addancin a jihar,” inji shi.

Daga nan ya bukaci duk wanda yake da wani bayani da ya tuntubi hedikwatar rundunar ko kuma ya kira lambobin kamar haka: 07015142112 08023871144.