Hukumar Tsaro Ta Farin Kaya (DSS), ta shawarci musulmin Najeriya da ke shirin bikin Ƙaramar Sallah da su lura da abin da ya shafi tsaro a filin Idi da sauraron wuraren shagulgula da za a yi a ranar Laraba, 10 ga Afrilu, 2024.
Rundunar jami’an tsaron sirrin ta kuma shawarci al’umma da su kai rahoton duk wani motsi da ba su yarda da shi ba ga jami’an tsaro, domin kaucewa fada wa tarkon masu tayar da zaune tsaye.
Haka kuma, hukumar ta ce za ta yi aiki kafada da kafada da rundunar ‘yan sandan Najeriya da sauran hukumomin tsaron ƙasar nan domin ganin an gudanar da bukukuwan Sallah lafiya.
A yammacin ranar Litinin ɗin da ta gabata ne dai Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar II ya bayyana cewa, ba a ga watan Shawwal ba a Najeriya, saboda haka za a yi hawan idin Karamar Sallah a ranar Laraba 10 ga Afrilu, 2024.
A sakonsa na bikin karamar Sallah, kakakin Hukumar DSS, Peter Afunanya, ya buƙaci ‘yan Najeriya da su ci gaba da zaman haƙuri da juna.
“Ina shawartar kowa da ya kasance mai lura da harkokin tsaro, sannan kowa ya zama yana iya gani ya fahimci abin zargi, sannan ya san yadda zai kai rahoto ga jami’an tsaro.”
Afunanya ya jaddada cewa, “Hukumar DSS na taya al’ummar Musulmi murnar bukukuwan karamar Sallah, tare da taya su murnar kammala azumin watan Ramadan cikin kwanciyar hankali.”
Ya ce lokacin azumi, lokaci ne na ibada, addu’o’i da kuma tuna girman Allah
“’ina rokonku da a cigaba da nuna irin dabiun da ka nuna lokacin azumi na zaman lafiya, jituwa da karimci”
Yayin da ake gudanar da wannan gagarumin biki na farin ciki, Hukumar ta bukaci a yi shagulgula cikin gaskiya da riƙon amana.
Hukumar DSS ta buƙaci ‘yan Najeriya su maida hankali wurin gudanar da ayyukan jin kai, tausayawa da hadin kai fiye da bukukuwa, ta kuma bukaci a kaurace wa duk wani abu da zai iya lalata zamantakewa.