Jakar kwalliya karamar jaka ce wadda za ki iya adana kayan kwalliyarki kamar; jambaki da gazal da hoda da sauransu.
Akwai abubuwa da dama wadanda suka cancanta ki sanya a jakar kwalliyarki don inganta adonki.
Amfani da jakar kwalliya wajibi ne ga mace domin kuwa wata ba za ta ganu ba in babu ita.
Kwalliya tana rufe tabon da ke fuska ko kurajen fuska; saboda haka in har ba ki da ita toya kamata ki samu.
A yau na kawo muku abubuwan da suka kamata jakarku ta kunsa:
- Concealer: Tana boye tabon da ke fuska.
A shafa ta bayan an shafa hodar fandesho.
- Maskara: Akan yi amfani da ita don taje gashin ido da sanya masa launi.
Akwai sababbin launuka na maskara a kasuwa wadanda za ki iya saya don kara wa gashin idonki kyau.
- Gazal: Shafa gazal a ido yana kara masa haske.
- Jambaki da man lebe: Suna kara kyau da kuma sanya lebba laushi.
Ki zabi jambakin da ya dace da launin fatarki domin inganta adonki.
- Fandesho: Idan mace ta yi alwala kwalliyarta za ta wanke musamman idan tana da kurajen fuska.
Wannan fandesho amfaninsa shi ne boye tabon kurajen fuska sannan yana kara hasken fata.
Yana da muhimmanci a samu fandesho a jakar kwalliya.
- Hoda: Bayan an shafa fandesho sai a shafa ta.
Tana tsotse gumin fuska da kuma sanya kwalliya ta dawo sabuwa.
Ya kamata a same ta a jakar mace.