✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kama matar da ke kai wa Bello Turji makamai a Zamfara

An kama matar ne da wani abokin tafiyarta ɗauke da wasu makamai a hanyar Zamfara.

Dakarun Rundunar Sojin Operation Fansar Yamma, sun kama wata mata mai shekara 25 a Jihar Zamfara, ɗauke da alburusai 764 da bindigogi guda shida, da ake zargin za ta kai wa ƙasurgumin ɗan bindigar nan, Bello Turji.

A cewar wata sanarwa da kakakin rundunar, Laftanar Kanal Abubakar Abdullahi ya fitar, an kama matar tare da wani abokin tafiyarta ne a ranar 28 ga watan Disamba, a yankin Badarawa, a Ƙaramar Hukumar Shinkafi.

Wannan na zuwa ne bayan samun rahoton sirri kan safarar makamai daga hanyar Kware zuwa Badarawa.

Dakarun sojin sun kafa shingen bincike a hanya, wanda hakan ya kai ga cafke waɗanda ake zargin.

Rundunar ta tabbatar da cewa a halin yanzu ana ci gaba da bincike a kansu domin gano cikakken bayani kan lamarin.

Sanarwar ta ƙara da cewa rundunar tana ƙudurin ganin ta daƙile safarar makamai zuwa hannun ’yan bindiga.

Hakazalika, ta roƙi jama’a su ci gaba da ba da sahihan bayanai domin taimakawa wajen samun nasarori irin wannan.

A baya dai ana zargin wasu mutane suna safarar makamai zuwa hannun ’yan bindigar da ke aikata miyagun laifuka a Zamfara da sauran yankunan Arewa Maso Yamma.

A watan Nuwamban da ya gabata ne, rundunar ’yan sanda ta kama wani ɗan ƙasar Aljeriya, mai shekara 58, da ake zargi da safarar bindigogi daga ƙasashen waje zuwa Jihar Zamfara.

Haka nan, an ƙwato bindigogi ƙirar AK-47 guda 16 a hannunsa, da wasu makamai daga wani mai ƙera bindigogi a Jos, a Jihar Filato ya ƙera.

Rundunar ta jaddada cewa za ta ci gaba da tashi tsaye wajen yaƙi da ’yan ta’adda da masu taimaka musu, har sai an samu zaman lafiya mai ɗorewa a yankin.