Ofishin jakadancin Saudiyya a Najeriya ya bayar da sanarwar rasuwar jakadan kasar a Najeriya Adnan bin Mahmoud Bostaji a yau Talata.
Majiyarmu ta samu rahoton cewa, kwanan ne iyalan Jakadan suka koma Saudiyya inda shi kuma yake Najeriya.
Rahoton ya kara da cewa, a daren yau Talata za a tafi da marigayin kasar Saudiyya.
Jakadan ya soma aiki da ma’aikatar harkokin wajen Saudiyya a shekarar 1991, a wannan shekara ne kuma aka nada shi a matsayin jakadan Saudiyya a Tehran wato babban birnin Iran, inda ya ci gaba da aiki har zuwa 1998.
Sannan ya kuma taba zama wakili a majalisar hada kan kasashen Gabas Ta Tsakiya tun daga 1998 har zuwa 2000.