Da fata an yi zabe lafiya, inda kuma ba a kare ba, muna addu’ar Allah Ya sa a gama lafiya kamar yadda muka kammala lafiya a Jihar Kaduna kuma Allah Ya ba ku shugabanni nagari kamar yadda muka samu a Kaduna.
Na shigo wannan fili ne domin in bayyana godiya ta musamman ga mutanen Kaduna, musamman matasa bisa yadda muka fito muka nuna wa duniya cewa muna tare da Malam Nasiru Ahmad El-Rufa’i. El-Rufai Gwamna ne jajirtacce, wanda ya san ya kamata. Hakan ya sa wasu jihohi suke shauki tare da fatan ina ma a ce miyar ta gidansu ce.
Iyaye da dama kullum matsalarsu ba ta wuce matsalar biyan kudin makarantar ’ya’yansu ba, amma El-Rufa’i ya dauke musu wannan, sannan ya ba yaran abinci mai inganci domin karatu bai yiwuwa da yunwa. Sannan aka kara musu da kayan makaranta.
A bangaren gina kasa kuwa ba a cewa komai, domin takwarana babu garin bai rusa ya gyara ba. Sannan aka gyara kananan asibitocin jihar. Ko a nan unguwarmu ta Hayin Banki, Karamar Hukumar Kaduna ta Arewa abin mamaki wai yau ga shi muna zuwa asibitin gwamnati na Hayin Banki! Wannan ai ba karamin abin murna ba ne.
Wadannan abubuwa da wasu ne suka sanya muka sake zaben Gwamna Malam Nasiru El-Rufa’i domin ya ci gaba duk da cewa wadansu ’yan adawa da ’yan ba-ni- na-iya sun yi ta kokarin ganin hakan bai yiwu ba.
Sannan jajircewarsa ba nan tsaye ba domin mutum ne ‘mayaki’. El-Rufa’i ya taimaka mana wajen kawo mana sababbin sanatoci wadanda muke so, kuma suke sonmu. Da kuma ’yan Majalisar Wakilai hazikai. Wannan ne ya sa a zaben muka yi SAK tun daga kasa har sama.
A Jam’iyyar APC babu munafunci ba son kai. Son jama’a shi ne ke zuwa a farko. Wannan ne ya sa El-Rufa’i ya zama daban. A sauran jihohi da ake fafutika da ’yan adawa masu yawa da karfi, sauran duk sun gigice, wadansu kuma suna cikin tashin hankali, amma shi kuwa har barcin hutu ya yi. Wannan alama ce ta yarda da kai, da kuma sanin abin da ka shuka, domin Hausawa na cewa abin da ka shuka shi za ka girba.
Haka sauran masu adawar ma da ’yan jam’iyyar hamayya kowa ya girbi abin da ya shuka ne ba dadi ba kari. Shi ya sa yake da kyau a rika bin liman da kyau, musamman idan ka san ba ki iya Sallar da kyau ba, ballantana ka ja Sallar da kanka.
A nan ne nake taya zababben Sanatanmu wato Uba Sani, da dan Majalisar Wakilai Malam Sama’ila Sulaiman farar aniya, da dan Majalisar Jiha mai wakiltar Kawo, Malam Aliyu Haruna Chakis da sauran takwarorinsa, da shugabannin jam’iyya baki daya da mu matasan jam’iya masu yi mata hidima da gwagwarmaya ba dare ba rana murnar samun nasara.
Haka kuma Shugaban Karamar Hukumar Kaduna ta Arewa shi ma ya nuna bajinta kwarai da gaske. Da kuma Kansilan mazabata ta Hayin Banki/Unguwar Kanawa/ Farin Gida Malam Danladi da shugabannina da iyayen jam’iyya na Hayin Banki, ina taya murna. Allah Ya maimaita mana.
A karshe nake kira mu ci gaba da hada kanmu tare da yi wa mutane hidima kamar yadda aka san Jam’iyyar APC da son mutane da yi musu hidima.
Daga Nasiru Ibrahim (Nasi), Hayin Banki Kaduna 08068611092.