Wani fitaccen lauya Barista Innocent Nkemjika Ezuego ya ce jahilci na daga cikin manyan dalilan da ke sanya mutane shiga kungiyoyin ta’addanci a kasar nan.
Barista Nkemjika Ezuego ya bayyana haka ne yayin da yake tattaunawa da Aminiya a karshen makon jiya a Abuja.
Ya ce rashin ilimi ne ke sanyawa ’yan ta’adda ke rudar jahilai su shiga cikin kungiyoyinsu. “Abu ne mai sauki a cusa gurbataccen ra’ayi ga jahili. Cikin sauki za a iya jan ra’ayin jahili a nuna masa cewa ta hanyar kashe mutum zai samu tikitin shiga Aljanna kai-tsaye,” inji shi.
Ya bayyana cewa hakan na faruwa ne saboda shi jahili ba zai iya karanta Alkur’ani ba har ya bayar da fassarar da ta dace.
Ya ci gaba da cewa jahili yana dogara ne da ra’ayin wadanda yake ganin su ne jagororinsa dangane da ayyukan ibadar da zai yi.
Barista Zuego ya kara da cewa matsalar ta’adanci da kasar nan take fuskanta ta faru ne saboda rashin jagoranci nagari.
Daga nan sai ya ce ya zama wajibi ’yan Najeriya su yi watsi da son zuciya su tabbatar da sun kawo canji ta yadda za a samu shugabanni nagari.
Ya bayyana cewa rashin shugabanci nagari na jawo satar kudin al’umma da yi wa shugabanni makauniyar biyayya da kuma rayuwa mai tsada da shugabannin suke yi.
Sannan kuma ya dora alhakin ta’adanci ga cin hanci da rashawa da take doka da oda da kuma rashin aikin yi.
Daga karshe sai ya ce bunkasa ilimi da saukaka shi tare da samar da ayyukan yi da samun shugabanni nagari na daga hanyoyin da za a yi maganin ta’adanci.
Jahilci ne ke sanya mutane shiga kungiyoyin ta’addanci – Lauya Ezuego
Wani fitaccen lauya Barista Innocent Nkemjika Ezuego ya ce jahilci na daga cikin manyan dalilan da ke sanya mutane shiga kungiyoyin ta’addanci a kasar nan.Barista…