✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Izala ta sake kai dauki ga ‘yan gudun hijira a Abuja

A ranar Lahadin da ta gabata ne kungiyar Jama’atu Izalatul Bid’a Wa ikamatissunnah (JIBWIS) ta sake kai dauki ga dubban ‘yan gudun hijira dake sansanoni…

A ranar Lahadin da ta gabata ne kungiyar Jama’atu Izalatul Bid’a Wa ikamatissunnah (JIBWIS) ta sake kai dauki ga dubban ‘yan gudun hijira dake sansanoni daban-daban a yankin Abuja a karo na uku cikin watanni biyu.

Kamar sauran lokutan na baya, ‘yan gudun hijirar sun samu tallafin buhunan shinkafa ne fiye da buhuna 500, wadda jimillan buhunan da aka raba din sun haura buhu dubu guda domin sakakawa al’ummomin da rikici ya rabo su da garuruwan su, sannan suke cikin gararin talauci, rashin matsuguni da rashin tabbas.

Babban Limamin Masallacin Juma’a na Shelkwatar kungiyar dake Utako a birnin tarayya Abuja, Imam Abdullahi Umar Adam ne ya jagoranci ayyukan rabon shinkafar ga ‘yan gudun hijirar da suka hada da Deidei, Dakwa, Apo, Wasaa, Durmi da Waru da sauransu, inda daruruwan ‘yan gudun hijirar ke rarrabe a kwangwaye da bacoci mafi yawansu mata ne da kananan yara.

A yayin da yake zantawa da wakilinmu jim kadan bayan kammala rabon abincin, Imam Abdullahi Umar ya bayyana cewa wani bawan Allah shi kadai ya dauki nauyin wannan aiki, inda ya bukaci Izala ta taimaka masa wajen jagorantar mika ta fisabilillahi ga ‘yan gudun hijira wadanda ya ce ya samu labarin irin wahalar da su ke fama da ita. 

“Muna alfahi da irin jajircewar wannan bawan Allah, duk da halin da ake ciki da matsin tattalin arziki, amma haka ya daure ya rufe ido yake turo wadannan buhuna kamar yadda kuke gani ana rabawa bayin Allah, kuma abin sha’awa game da wannan aiki shi ne yadda ya bukaci mu boye sunansa, y ace ya na yi ne ba don kowa ba, ba don neman yabon kowa ba, ba don neman yardarm kowa ba, yana yi don neman yardarm mahiliccinsa wanda kuma Ya ba shi ikon aiwatar da wannan aiki.”

Haka kuma malamin ya kara da cewa, wannan wani bangare ne na shirin kungiyar Izala don tallafawa marayu da ‘yan gudun hijiran, wadda wannan shine karo na uku a cikin watanni biyu kacal. Sannan sai ya yi kira ga Attajirai da su rika yin koyi da irin wadannan bayin Allah wajen tallafawa mabukata a fadin kasar nan, musamman ma marayu, zawarawa da ‘yan gudun hijira.