Iyayen da aka sace ’ya’yansu a Kano sun zargi gwamnaitn jihar da yin watsi da su da kuma kin kwato ’ya’yansu da aka gano a Jihar Anambra.
Kungiyar iyayen yaran da aka sace Kano (PATAMOOC) ta ce yaran da aka gano su 18 a Jihar Anambra har yanzu ba kawo su Kano ba, domin gano iyensu da kuma mika musu su ba.
- Rikicin daukar ’yan sanda 10,000 ya kara kazancewa
- Abubuwan da ya kamata ku sani a kan ranar Hausa ta Duniya
Sun zargi Gwamantin Ganduje da yin watsi da su da kuma kin yin komai kan rahoton kwamitin da ta kafa kan gano yaran da aka sace daga 2010 zuwa 2019, bayan an mika masa rahoton a 2021.
“Abin da muke cewa shi ne a sake bibiyar wannan batun [da ka yi watsi shi] ganin halin da iyaye da dangi da kuma mambobin wannan kungiya ke ciki” in ji Isma’il.
Don haka suka yi barazanar kaurace wa zaben 2023 idan gwamnatin jihar ba ta kwato ’ya’yan nasu ba.
Kungiyar na da mambobi sama da 200 wadanda iyaye ne da aka sacewa ’ya’yansu.
Wadansu daga cikin iyayen yaran da aka sace sun shiga hali na rashin lafiya sakamakon damuwa da tashin hankali, in ji Isma’ila a cikin sanarwar.