Yayin da halin da aka shiga a kasar Afghanistan yake kara tsananta, iyaye a kasar sun fara sayar da wasu daga cikin ’ya’yansu domin samun kudin abincin ciyar da wasu ’ya’yan.
Rahotanni sun ce ’yan watanni bayan karbar mulkin Taliban a kasar, akalla mutum miliyan tara ne suka fada cikin matsanancin talauci.
- Yadda Taliban ke yaki da shan miyagun kwayoyi a Afghanistan
- Hankalina ba zai kwanta ba sai na gaji Buhari a 2023 — Yahaya Bello
Wakilin BBC a kasar, Yogita Limaye, ya tattauna da wata uwa wacce ta sayar da jaririyarta a kan Dalar Amurka 500 domin samun kudin ciyar da ragowar ’ya’yan nata.
Wanda ta sayi jaririyar dai ba a bayyana sunansa ba, kuma ba a san me zai yi da jaririn ba, ya yi ikirarin cewa yana son ya raineta ne saboda ta auri dansa idan ta girma.
Ya dai biya Dala 250 ne a nan take, kudin da za su ishi iyalan su sayi abinci na tsawon watanni, inda ya yi alkawarin cika ragowar da zarar ya karbi jaririyar lokacin da ta fara tafiya.
Mahaifiyar dai ta ce, “Yunwa na barazanar kashe ragowar ’ya’yana, ya zama tilas na sayar da wannan jaririyar.
“Amma tabbas na damu matuka saboda ita ma ’yata ce, ba yadda zan yi na sayar da ita inda ina da wata hanyar,” inji mahaifiyar, kamar yadda ta shaida wa BBC.
Shi kuwa mahaifin jaririyar, wanda ke sana’ar kwashe shara amma ya gaza samun kudi a tsawon lokaci shi ma ya ce sun dauki matakin ne saboda ba su da wani zabi.
Ya ce, “Muna cikin yunwa. Yanzu haka ba mu da ko kwayar hatsi ko man girki a gidanmu. Ba mu da komai!
“’Yar tawa ba ta san yadda makomarta za ta kasance ba, ban san yadda za ta karbi labarin haka ba a nan gaba, amma dole ce ta sa muka yi haka.”
A kasar Afghanistan dai a kan aurar da mata da wuri, to amma yanzu matsin tattalin arziki ya sa iyalai da dama sauya salo.