Hajiya Jummai Idris Muhammed ita ce Babbar Sakatariya a Ma’aikatar Ilimi ta Jihar Neja. Duk da yake daga farko ta samu gurbin karatu ne a fannin girke-girke da yawon bude-ido a Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya, daga baya ta zama ma’aikaciyar asibiti a bangaren jinya bayan ta bi shawarar mijinta. Ita ce ta biyu a wajen marigayi Jakada Idris Muhammed Ja’agi kuma an haife ta ce a 1964. A tattaunawarta da Aminiya ta bayyana irin gwagwarmayar da ta sha a rayuwa kamar haka:
Neman Ilimi:
Tun da farko na fara karatu ne a kauyen Ja’agi da ke Karamar Hukumar Mokwa a Jihar Neja. Daga bisani mahaifina ya koma da ni Sakkwato inda na shiga makarantar firamare ta Danbaba Marafa a 1971. A can na yi ajin firamare na daya zuwa na hudu daga nan kuma sai na koma Jihar Neja a 1976 inda na shiga makarantar firamare ta Waziri inda na kammala ilimin firamare dina.
A lokacin da na shiga ajin farko na makarantar gaba da firamare a tsakanin 1977 zuwa 1978, cikin rashin sa’a sai na yi rashin lafiya wadda ta sanya aka mayar da ni Kwalejin ’Yan mata (WTC), Minna, inda na samu horo na shekara biyar a fannin koyarwa. A can na samu shaidar malama mai daraja ta biyu (Grade II). Daga nan na samu shiga Jami’ar Ahmadu Bello ta Zariya don karanta Girke-Girke da Yawon Bude-Ido (Catering and Tourism). To sai dai kuma mijina ba ya son wannan fanni da zan karanta, shi yana so ne in zamo malamar jinya wato Nas. Na yi aure tun ina karatun sakandare domin a lokacin ina karama, shi kansa mijina jami’in jinya ne, don haka sai ya turo mini manya daga cikin abokan aikinsa don su zo su ba ni shawara in rungumi harkar karatun jinya.
Tunda na karanci wasu darussan kimiyya a matsayina ta malama a ganinsu karatun jinya ba zai yi mini wahala ba. Duk da yake ba ni da sha’awar yin karatun amma saboda daraja aure sai na amince da haka. Burina shi ne in samu ingantaccen ilimin boko don tun ina karama idan na ga makwabtanmu wadanda suka yi ilimin boko suna burge ni har nakan yi fatan idan na girma in zama fiye da yadda na ganSu.
Kasancewar mahaifina jami’in diflomasiyya, na kudiri aniyar wata rana sai na zama Sanata. Niyya a kan kaina wata rana zan zama Sanata don ina so in ceto al’umma musamman mata daga kangin da suke ciki. Saboda haka burina shi ne in yi karatun da zan taimaki al’umma musamman mata da marasa galihu.
A 1983 ne na samu gurbin yin karatu a Kwalejin Koyon Aikin Jinya. Da yake sun yi wata uku da fara karatun kafin in shiga ban yi tsammani zan iya kaiwa ga gaci ba, amma Allah cikin ikonSa Ya taimake ni na ci jarrabawa. Na yi sa’a don duk wanda bai yi nasarar cin jarrabawar ba, korarsa ake yi.
Na kammmala makarantar aikin jinya wato Nas a 1986 a matsayin ma’aikaciyar jinya mai rajista. Da yake babu wani aiki da za a ba ka da zarar ka gama sai na shiga neman aiki. A wancan lokacin an kaddamar da Hukumar Gudanarwar Asibitocin Jihar Neja ta farko don, haka su ne na farko da suka fara gayyatarmu don yi mana jarrabawar daukar aiki, a lokacin ina dauke da cikin dana na uku. A lokacin da na samu aiki ina da tsohon ciki don haka ba dama in fara aiki. Abin takaici ne amma a haka na yi hakuri har sai da na haihu a 1987, sai a watan Afrilun 1988 na fara yin aiki.
A 1992 ne na kara kaimi na yin kwas din ungozoma tunda ina da burin yin haka kasancewata jami’ar jinya. Don haka sai na shiga Makarantar Ungozoma ta Minna (School of Midwifery). Da na kammala sai hukumar makarantar suka fahimci cewa ina da kwarewa a fannin koyarwa don haka suka nuna suna son su rike ni, amma ni kuma ban gamsu da haka ba, dominina so ne in yi abin da na koya a aikace. Daga nan ne sai na koma Babban Asibitin Bidda inda na fara aikin ungozoma domin sha’awata da son taimaka wa mutane.
Mukaman da na rike:
Na yi digiri na biyu a bangaren Harkokin Mulki daga shekarar 2012 zuwa 2013. Na rike mukamin Rajistara tare da kasancewa malama a Makarantar Ungozoma ta Minna a Jihar Neja. Sannan na taba rike mukamin Daraktar Bincike da Kididdiga a Hukumar Kula da Lafiya a Matakin Farko (PHCDA). A halin yanzu kuma ina rike da mukamin Babbar Sakatariya a Ma’aikatar Ilimi ta Jihar Neja.
Kalubale:
Kalubalen da ake fuskanta a wajen aiki ba za su iya kirguwa ba. Wannan ne dalilin da ya sanya ake son mutum ya samu cikakken horon da ya kamata a kan duk irin aikin da yake gudanarwa da bin dokokin aiki ba tare da ketare iyaka ba, wanda hakan kan iya janyo maka matsala. Bayan da na karanci fannin ilimin shugabanci da lokacin karin girma ya zo sai wadansu suka rika rade-radin ba zai yiwu a kara mini girma ba, saboda asalin layina shi ne aikin jinya amma saboda aiki tukuru da kuma kwarewata sai aka yi mini karin girma.
Sannan akwai kalubale a kullum a tsakanin abokan aiki. Ba ma kamar idan an zo wajen maganar cin nasara a rayuwa. Don haka kada ka amince wa kowa a kan kudirorinka na kaiwa ga nasara, kai dai ka bar shi a tsakanin kai da Ubangijinka. Domin kuwa watakila mutumin da kake ta hakilon labarta masa tsare-tsarenka, ba masoyinka ba ne, ko shi ma yana da irin wannan buri, kai dai ka kasance mai kiyaye duk abin da za ka fada da kuma ayyukanka. Sannan ka kara da hakuri da yin addu’a to za ka cimma nasara.
Wani kalubale da na fuskanta kuma a rayuwa shi ne zabi ga aure. Kamata ya yi iyaye su bar ’ya’yansu su zabi wanda suke so su aura. Ba ma kamar yanzu da yake zamani ya canja. Domin kuwa haka ta faru a gare ni kuma har yanzu abin yana raina. Iyayena ne suka zaba mini mijin aure, kuma a lokacin ban samu ta cewa ba domin neman albarkarsu. Saboda ina yarinya ’yar sakandare aka yi mini aure wanda haka ya sanya ni cikin wahala matuka ganin cewa ga shi na hada karatu da kuma rainon iyali a lokaci guda.
Iyali:
Na fito ne daga Karamar Hukumar Mokwa a Jihar Neja. Kuma ni ce ta biyu a gidanmu. Da yake wanda yake na fari a gidan an ba da rikonsa a kauye, wannan ya ba ni damar in kasance kamar ni ce babba a gidan. Ina da kanne da dama da ni nake daukar dawainiyarsu duk da yake iyayenmu suna raye. Amma tunda yake ni ce babba ya zama tilas gare ni in taimaki iyayena wajen dauke msuu wani nauyin. Saboda haka wannan ne ya sanya na kasance shugaba tun asali.
Sannan a matsayina na mai kwazo da hazaka na rike mukamai masu yawa tun a makaranta. Kamar shugabar aji, shugabar kula da dakin kwana na dalibai da kuma shugabar sashen kula da abincin dalibai.
Darussan da na koya a rayuwa:
Ana koyon darussa a rayuka a kusan kowane mataki. Ka ga dai an yi mini aure ina ’yar karama a lokacin ban ma san mene ne auren ba. To amma tunda yake abin da iyayena suke so ke nan dole na bi su. Haka na yi a matsayin ’yar shekara 19. Na koyi darussa na rayuwa masu tsanani a wancan lokaci, wadanda su ne suka sa na cimma burina a yau. Na haifi dana na fari tun ina makarantar gaba da firamare, ka ga, ga karatu kuma ga raino. A haka kuma na kammala na jajirce sai na ci gaba da karatu. Hakan ya sanya iyayena suka bukaci mijina lallai sai ya bar ni na wuce mataki na gaba. Da hakan ba ta faru ba watakila da ban kasance inda nake ba a yau. Duk da yake abu ne da ya kasance mini babban kalubale wato na samun ’ya’ya tun ina karama, amma ilimi musamman ga mace yana da matukar muhimmanci. Haka ya sanya ni da ’ya’yana muka girma kamar sa’o’in juna. Ina faman tarbiyyantar da kaina kuma a waje daya ina tarbiyyar ’ya’yana. Don haka na fuskanci kalubale sosai tun daga farkon rayuwata. A cikin shekara biyar na samun takardun shaidar kammala karatu daban-daban.
Rayuwa a lokacin da nake karama:
Tun asali ni ba mai son yin kawaye barkatai ba ce. Ina da kawaye biyu ne kacal kuma iyayenmu ma sun san junansu. Daya daga cikin kawayen nawa ta rasu amma dayar tana nan a raye kuma har yanzu muna zumunci. Ni ban iya ko gardama ba, in dai ka gan ni ina gardama to kuwa a kan wani abu ne muhimmi.
Mafi kololuwar mukami:
Mafi kololuwar mukamin da na samu a matsayina na ma’aikaciya shi ne mukamin Babbar Sakatariya a Ma’aikatar Ilimi ta Jihar Neja a ranar 1 ga watan Nuwamban 2018. Kuma kamar yadda na fada a baya a dukkan wani mataki da ka taka a rayuwa kana samun kalubale amma dai idan ka jajirce to daga karshe za ka kai ga gaci. Kuma duk irin halin da ka tsinci kanka a ciki za ka samu mutanen da sun aminta da abin da kaske yi. Zama Babbar Sakatariya a Jihar Neja abu ne da ban taba tsammaninsa ba. Amma ya zo mini kamar a mafarki. A shekarar 2010 tsohon Gwamnan Jihar Neja Dokta Muázu Babangida Aliyu ya zabe mu mu 28 ya ce a nan gaba za mu zamo manyan sakatarori don haka sai ya tura mu mu je mu yi digiri na biyu. Ni na yi nawa digirin na biyu ne a fannin shuganci wato Public Administration a tsakanin shekara 2012 zuwa 2013. Sai dai kuma a wancan lokacin ban yi sa’ar shiga cikin wadanda aka zaba ba sai yanzu. Don haka na yarda idan dai da hakuri da kuma imani, to za ka iya cimma burinka kowane iri ne.
Fatata a rayuwa lokacin da nake karama:
Fatata a rayuwa sa’ar da nake karama ita ce in taimaka wa marasa galihu don su kasance suna da tagomashi kamar kowa. Har kullum ina son in taimaki wanda yake cikin kunci.
Farincikin kasancewa uwa
Ina da ’ya’ya hudu. Burina shi ne in taimaka musu su ci nasara a rayuwarsu da kuma iliminsu. Farin cikina a matsayina na uwa shi ne in taimaka musu su yi abin da ya wuce wanda ni na yi a yanzu. Kuma a halin yanzu ina farin cikin ganin yadda na samu nasarar tarbiyantar da su. A halin yanzu dukkansu sun kammala karatun jami’a. Daya daga cikin ’ya’yana ta karanta fannin shugabanci (Public Administration). Dana na farko ya karanta fannin kididdiga (Statistics), sannan ya yi digirinsa na biyu a fannin Tattalin Kudi (Financial Economics). Na biyu yana da digiri a fannin sinadarai (Chemistry) shi kuma na ukun yana da digirin farko a fannin tsimi da tanadi wato Economics, da kuma digiri na biyu a fannin tsimin kiwon lafiya (Health Economics). To ka ga wannan ya yana sanyaya mini rai kuma yana sanyawa inji na cimma burina a matsayina na ’yar shekara 54. Biyu daga cikinsu suna aiki, su ma sauran biyun suna daf da samun nasu ayyukan. Don haka ko yanzu ta Allah ta yi na san za su iya rike kansu da kansu.
Yadda na hadu da mijina:
Aurena aure ne da iyayena suka yi mini.
Abubuwa biyar da na fi so:
Rayuwa mai kyau da koshin lafiya. Ban da wani buri baya ga in ga ’ya’yana sun girma. Na kuma koyar da su tarbiyya tagari kamar yadda kowace uwa tagari ya kamata ta yi, kuma wannan ita ce hanyar da ya kamata su bi.
Sannan kuma hakki ne da ya rataya ga iyaye su bai wa ’ya’yansu mata dama su yi karatu don a samu al’umma tagari a nan gaba. Nauyi ne a kan dukkan iyaye su ciyar tare da tufatar da kuma ilimantar da ’ya’yansu domin a samu al’umma tagari a nan gaba. Sannan duk wanda ya ilimantar da ’ya mace ai kamar ya ilimantar da kasa ne baki daya.
Manhajar sadarwa da nake fara dubawa da safe ko kafin in kwanta barci:
Koyaushe nakan duba manhajar WhatsApp da safe da kuma dare kafin in kwanta domin duba muhimman sakonnin da ka iya shigowa.
Kayan kwalliya
Ina son kayan ado na kawa sosai.
Suturar da ba za a taba ganina da ita ba:
Kaya masu nuna tsiraici
Inda na fi son kai ziyara da dalili:
Ina kai ziyara Dubai saboda kyawunta.
Yadda nake hutawa:
Nakan huta ne ta hanyar motsa jiki daga nan kuma sai in yi barci.
Abincin da na fi so
Ina son tuwon shinkafa da miyar wake (gbegiri)
Shawarar da mahaifiyata ta taba ba ni da har yanzu take a raina:
A koyaushe shawarar mahaifiyata ita ce ki yi aiki tukuru sannan ki yi hakuri a duk irin yanayin da kika tsinci kanki a ciki.
Idan na tuna baya shawara da zan ba matasa:
Ina son in fada musu cewa a koyaushe su jajirce kada su taba samun mutuwar zuciya a kan wani abu da suka sanya a gaba. Domin kuwa babu wani abu da yake samuwa da sauki a rayuwa. Don haka kafin ka kai ga gaci sai ka samu kalubale iri daban-daban.
Shawarata ga mata:
Su bai wa ’ya’yansu tarbiyya, da kwarin gwiwa da kuma zaburar da su a kan neman ilimi. Ba ma kamar ’ya’ya mata. Sannan kada su tursasa wa ’ya’yansu mata yin auren wuri.