Iyalan gidan shugaban kungiyar Yarbawa zalla ta Afenifere Cif Reuben Fasoranti sun karyata jawabin Kwamishinan ‘yan sandan jihar Ondo Undie Adie, wanda ya ce ba Fulani makiyaya bane suka kashe ‘yar shugaban Afenifere ba, domin zuwa yanzu ba a kai ga gano wadanda suka yi aika-aikar ba dan haka babu wanda zai iya cewa wane ne ya yi, “‘yan bindiga ne da suka tsare hanya suka bude wuta akan matafiya, mun dauki kwararran matakan ganin an kamo wadanda suka yi aika-aikar domin su fuskanci hukunci.” In ji shi.

Kwamishinan ‘yan sandan ya bayyana haka ne a zantawar sa da manema labarai a harabar gidan shugaban kungiyar Afenifere da ke Akure a jihar Ondo, jawabin da kanin marigayiyar Kehinde Fasoranti ya karyata a lokacin da yake zantawa da ‘yan jaridu a madadin iyalan gidan su, ya ce ya halarci ofishin ‘yan sanda mafi kusa da wajen da lamarin ya faru wadanda suka shaida masa Fulani makiyaya ne suka kashe ‘yar uwar ta su.
Kisan ‘yar shugaba kungiyar Yarbawa zalla ta Afenifere Olufunke Olakunrin ya tada kura inda ya janyo cece kuce bayan da aka alakanta shi da Fulani makiyaya lamarin da ya sanya shugaban kungiyar Yarbawa ta OPC Gani Adams, yin gargadin cewa, kada a zarge su akan abin da zai biyobayan martanin su akan lamarin.