Iyalan ’yan sanda 19 da suka rasu a bakin Jihar Gombe sun karbi cekin kudi Naira miliyan 80 a matsayin hakkokinsu.
Kwamishinan ’yan sandan jihar, Hayatu Usman, ya jinjina wa ’yan sandan da suka kwanta dama.
Ya ce ba za a taba manta gudummawarsu ba da kuma yadda suka sadaukar da rayuwarsu ga kasarsu.
Kwamishinan ya yi addu’ar samun rahama, ya kuma bakaci iyalan su ci gaba da yi musu addu’a a kodayaushe.
- Farfesan da ke sana’ar walda a gefen titi
- Kisan ’Yan Mauludi: Bala’in ya yi wa ’yan Arewa yawa —Bello Yabo
- Dan kasuwa ya nemi kashe matarsa don ya kara jari a shagonsa
Da yake mika wa iyalan cekin kudaden a hedikwatar rundumar, CP Hayatu ya shawarce su da su ririta abin da suka samu.
Kwamishinan ya mika wa iyalan cakin kudin ne a madadin shugaban ’yan sandan Najeriya, a karkashin shirinsa na kula da iyalan ’yan sanda.
Wakiliyar iyalan mamatan ta yi godiya ga rundunar bisa yadda ta biya su hakkokin mazajensu da ’yan uwansu domin rage musu wahalhalun rayuwa.