✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Iyalai biyar sun mutum sanadiyar cin shinkafa

Al’ummar kauyen Umuatuegwu da ke garin Okija a Karamar Hukumar Ihiala da ke Jihar Anambara sun ga tashin hankali yayin da iyalai biyar na zuriyar…

Al’ummar kauyen Umuatuegwu da ke garin Okija a Karamar Hukumar Ihiala da ke Jihar Anambara sun ga tashin hankali yayin da iyalai biyar na zuriyar Ndenemenu suka mutu sanadiyar sun ci shinkafa.
Marigayi Albert Ndenemenu wanda ke yin sana’ar achaba da matarsa Nwanne da ’ya’yansu uku sun mutu nan take.
Kodayake an samu rahotanni masu karo da juna dangane da abin da ya yi sanadin mutuwar tasu.
Yayin da wadansu ke zargin kasancewar guba a cikin abincin wadansu kuwa sun alakanta lamarin da  ketar matsafan da ke cikin dangin iyalan.
Aminiya ta gano cewa mahaifiyar marigayiya Nwanne wacce ita ta mutu daga karshe ta dafa shinkafar da iyalan za su ci da rana inda kowa ya ci, jim kadan mijinta da ’ya’yanta suka fara aman jini.
“Lokacin da mazauna kauyen suka iso gidan bayan da aka yi kururuwar neman ceto sai suk tarar duk sun mutu. Matar tana ganin gawar mijinta da ta ’ya’yanta sai kawai ta yanke jiki ta fadi nan take aka kai ta asibitin koyarwa na Nnamdi Azikiwe da ke garin Nnewi inda ita ma rai ya yi halinsa”. Inji majiyarmu.
Wani mazaunin kauyen wanda bai so a bayyana sunansa ba ya ce har kawo yanzu ba a tantance abin da ya yi sanadin mutuwarsu ba.
Ya bayyana cewa duk kokarin da aka yi don ganin hukumar asibitin Nnamdi Azikiwe sun gundar da gwajin gawar mamatan ya ci tura.
Aminiya ta gano cewa tuni ’yan sanda da ke garin Okija suka gayyaci ’yan’uwan mamatan uku don gudanar da bincike.
Mai Magana da Yawun Rundunar ’Yan sandan Jihar Anambara, Misis Nkiru Nwode ya tabbatar da aukuwar lamarin.
Nwode ya bayyana cewa tuni suka fara gudanar da bincike inda ya kara da cewa an dakatar da gudanar da gwajin gawar mamatan.