Mayakan ISWAP sun yi awon gaba da wasu matafiya 15 a wani sabon hari da kungiyar ta kai a Jihar borno.
Kungiyar ta sace matafiyan ne a wani shingen bincike da mayakanta sanye da kayan sojoji suka kafa a kusa da kauyen Gumsuri da ke Damboa lga a Karamar Hukumar Damboa ta jihar.
- Zulum ya dauki nauyin karatun marayun da Civilian JTF suka bari
- Hatsarin Bagwai: ‘Har yanzu muna neman gawarwakin mutum 14’
Wata majiyar tsaro ta ce, “Abin takaici ne yadda ’yan tayar da kayar bayan suka ci gaba da tafka ta’asarsu a yankin Dajin Sambisa; Mun samu rahoto cewa ISWAP ta yi garkuwa da matafiya kusa da kauyen Gumsuri, amma sun kyale mutum biyu daga cikinsu.
Majiyar ta bayyana cewa lamarin ya faru ne a ranar Laraba, bayan mayakan sun bi sawu matafiya suka yi awon gaba da su zuwa cikin Dajin Sambisa.
Yawancin mutanen da aka sace din matasa ne da suka baro garin Damboa a kan hanyarsu ta zuwa Jihar Adamawa.
Daga cikin matafiyan da kungiyar ta yi garkuwa da su din har da ma’akatan kungiyoyin agaji na kasashen duniya.