✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

ISWAP ta sace dan sanda da wasu mutum 7 a Borno

An kai harin ne da safiryar Asabar a Gubio

’Yan ta’addan kungiyar ISWAP sun kai wani harin bazata a jihar Borno, inda suka yi awon gaba da dan sanda da kuma yan sakai na rundunar CJTF guda hudu da mafarauta guda uku.

Maharan sun kai farmakin ne da sanyin safiyar Asabar a karamar hukumar Gubio da ke jihar ta Borno.

Bayanai na nuni da cewa an yi awon gaba da jami’an tsaron ne bayan da ’yan ta’addan suka mamaye inda suke da zama.

Majiyar ’yan sanda ta shaida wa Zagazola Makama, wani kwararre kan yaki da tada kayar baya kuma mai sharhi kan harkokin tsaro a Tafkin Chadi cewa an kai wa jami’an tsaron hari ne a wata RUGA da ke kauyen Pompom Baliya da ke da tazarar kilomita biyar daga garin Gubio.

’Yan ta’addan sun kuma dauke motar sintiri kirar Hilux guda daya da makamai sannan suka nufi kauyen Gadai da ke karamar hukumar Nganzai.