✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

ISWAP ta kashe mutum 30 a Dikwa

Mayakan sun yanka akasarin mutanen da suka kama.

Mayakan ISWAP sun kashe akalla mutane 30 a kauyen Mudu da ke Karamar Hukumar Dikwa a Jihar Borno.

Bayanai sun ce wannan hari na zuwa ne amatsayin ramakon kashe kwamandan su da sojoji suka yi ta hanyar kai harin sama a jihar.

Majiyoyi daga yankin sun shaida wa Kamfanin Dillancin Labaran Faransa AFP cewar mayakan sun kai hari ne a kauyen Mudu a karshen mako.

Wani shugaban ’yan sa-kai da ake kira Babakura Kolo a Maiduguri, ya bayyana cewa mayakan sun yanka akasarin mutanen da suka kama wadanda maza ne da ke kokarin tserewa daga yankin.

Kolo ya ce akasarin wadanda aka kashe ’yan gwangwan ne da ke neman karafa daga motocin da aka kona ko aka daina amfani da su a yankin saboda hare-haren mayakan Boko Haram bayan sun je kauyen daga Rann wanda ke da nisar kilomita 80 a tsakaninsu.

Wani shugaban ’yan sa-kai, Umar Ari ya ce mayakan ISWAP suna zargin wadanda suka kashen ne da bai wa jami’an tsaro bayanai game da harkokin su.

Rikicin Boko Haram ya yi sanadiyar hallaka mutane sama da 40,000 da kuma raba mutane sama da miliyan biyu daga muhallinsu tun daga shekarar 2009 kawo yanzu.