Kungiyar ISWAP mai tayar da kayar baya a Yammacin Afirka, ta haramta wa al’ummar garin Buni Gari da ke Jihar Yobe shiga yankin da ta yi sansani.
ISWAP wadda ta kashe mutum 10 na al’ummar garin a ranar Alhamis ta gargadi mazaunan da su kiyaye wannan umarni ko su fuskanci fushinta.
- An kai wa Firaministan Japan hari yana tsakar yakin neman zabe
- Zamanatar da kasuwancin kayan marmari ya janyo min bunkasa —Dankama Fruits
Wakilinmu ya ruwaito cewa wannan dai na kunshe ne cikin bayanan da kwararren mai fashin baki kan sha’anin tsaro da tayar da kayar baya a yankin Tafkin Chadi, Zagazola Makama ya fitar.
Makama ya ce gargadin na ISWAP na zuwa ne jim kadan bayan kammala jana’izar mamatan goma da ta kashe.
Ya bayyana cewa kungiyar ta yi gargadin ba ta son ganin kowa a yankin da mayakanta ke walwala a matsugunnin da suka kafa a Buni Gari.
An ruwaito cewa, gabanin harin hallaka mutane goman da ISWAP ta kai a kan babura da motoci kirar Hilux, sun soma shaida wa mazaunan yankin cewa kada su damu da kasancewarsu.
ISWAP dai ta kara jaddada gargadinta ga mutanen yankin kan kada su kwarmata wa jami’an tsaro ko wani irin bayani a kansu.
Aminiya ta ruwaito cewa mayakan sun ja kunnen mazauna yankin da su daina bayyana duk wasu sirraka nasu ga sojoji wanda a dalilin haka suke fuskantar matsim lamba na hare-hare.
Sai dai duk da wannan gargadi, mayakan sun rubanya jan kunnen ta hanyar dasa bama-bamai a wasu hanyoyin da ke yankin domin janyo koma baya wa ayyukan sojoji sanadiyyar hare-haren da suke kai musu.
Wata majiya da ke yankin ta bayyana wa Aminiya cewar, sansanonin ’yan ta’addan ba su da nisa daga garin na Buni Gari wadda hakan ya sa al’ummomin yanki ke fuskantar barazanar zuwa gonaki da zarar damina ta fadi musamman ta bana da ake zaman tsammaninta.
Dangane da wannan dalili ne mazauna yankin ke rokon jami’an tsaro da su kara kaimi bisa ga kokarin da suke yi don ganin sun samu damar fita gonakinsu cikin halin kwanciyar.