Kungiyar ISWAP da ke da’awar jihadi a Yammacin Afirka ta dauki alhakin harin da aka kai wa ofishin ’yan sanda da ke Adavi a Karamar Hukumar Okene a Jihar Kogi.
A safiyar ranar Asabar ce dai mahara suka far wa ofishin, inda jami’in hulda da jama’a na rundunar ’yan sanda reshen jihar ta Kogi William Aya ya ce maharan sun bude wuta ne kan mai uwa da wabi, da yayi sanadiyar rasa jami’an ’yan sanda uku.
- Matsalar Tsaro: Birtaniya ta horas da dakaru 145 a Najeriya
- Mazabar Bichi ta saya wa dan majalisa fom din neman tazarce
Ya kuma ce an samu musayar wuta tsakanin ’yan sandan da ’yan ta’addan wanda hakan ya sa suka ari na kare da kyar da raunuka.
Aya ya kuma ce Kwamishinan ’yan sandan Jihar CP Edward Egbuka ya samar da tawagar tsaro da za ta dinga sintiri a yankin domin tabbatar da aminci da zaman lafiya.
Muryar Amurka ce dai ta ruwaito cewa ISWAP a wata sanarwa da ta fitar a shafinta na Telegram ta dauki alhakin harin, inda ta ce ta yi nasarar halaka mutane biyar a farmakin.