Sojoji na shirye-shiryen dakile hare-haren da ake rade-radin kungiyar ISWAP na shirin kai wa wasu yankunan Jihar Borno a lokacin bukukuwan karshen shekara.
Wata majiyar tsaro ta ce mayakan ISWAP sun shirya kai hare-hare kan sansanonin soji da nufin kawar da hankalinsu daga shirin kungiyar na kai hari tare da sace ’yan mata masu yawa a kauyukan wasu kananan hukumomi biyu da ke kusa da Dajin Sambisa a ranar jajiberin Kirismeti.
- Muna binciken kisan fararen hula harin jiragen yaki a Zamfara —Sojoji
- Matashin da ya yi kisa kan butar shayi zai bakunci hauni
“Bayanan sun nuna cewa ISWAP ta kammala shiri tare da tattara mayaka don kai hari kauyuka a lokacin bukukuwan Kirsimeti da Sabuwar Shekara a kananan hukumomi biyu da ke yankin Kudancin Bornon.
“Sun tanadi manyan makamai, musamman bindigogin yaki da jiragen sama da kuma makamin roka,” in ji majiyar Aminiya.
Domin yin hakan, majiyar ta ce, sun shirya kai hare-hare kan sansanonin sojin da nufin karkatar da hankalinsu daga ainihin manufarsu.
Ta ce wannan ne ya sanya rundunar sojin ta daura damarar dakile shirin ’yan ta’addan da kuma tabbatar da an gudanar da bukukuwan lafiya.