Akalla mata da mayakan Boko Haram da ISWAP 55 ne aka kashe a wani artabu da kungiyoyin suka shafe mako guda suna yi a tsakaninsu a Jihar Borno.
Aminiya ta gano rikicin ya faro ne tun a makon da ya gabata, a wani sansanin ’yan ta’adda da ke Bama, inda ’yan Boko Haram da dama suka sheka lahira.
Wani da ke da masaniya kan aukuwar lamarin da ya nemi a sakaya sunansa, ya ce an kashe mayaka da sauran mutane da dama a wani fadan da shi ma suka yi a filin Dala da ke Dajin Sambisa a ranar Asabar.
Majiyar ta kara da cewa mayakan ISWAP sun rubanya na Boko Haram din, kuma 11 daga cikinsu ne suka mutu a artabun na yankin Mantari.
Da yake karin haske kan lamarin, wani kwararre a fannin yaki da tada kayar baya a yankin Tafkin Chadi, Zagazola Makama, ya ce mayakan da ke Sambisa sun so daukar fansa ne kan kashe wani kwamandansu, Malam Aboubakar (Munzir) da wasu mayakansu 15 a wani kazamin artabun na daban.
Ya ce a ranar Asabar, wani babban kwamandan Boko Haram mai kula da Tsaunin Mandara, Ali Ngulde, ya jagoranci daruruwan mayaka dauke da muggan makamai, suka gwabza da ISWAP a Dajin Sambisa.