Majiyoyin tsaro masu tushe sun tabbatar wa Aminiya cewa ’yan ta’addan kungiyar ISWAP da na Ansaru ne suka tarwatsa titin jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna da nakiya.
Majiyoyin sun tabbatar mana da hakan ne a ranar Alhamis, bayan hare-haren da aka kai wa titin jirgin kasan a ranar Laraba da dare da safiyar Alhamis sun jefa matafiya cikin tashin hankali, kafin daga basani Hukumar Sufurin Jiragen Kasa a dakatar da zirga-zirgar jirage daga Abuja zuwa Kaduna.
- Najeriya A Yau: Harin Jirgin Kasa ya ja wa Najeriya asarar N25m a kullum
- Sojoji sun kashe sabon shugaban ISWAP, Malam Bako
Hukumar dai ta zargi bata-gari masu satar karafunan da yin danyen aikin, amma majiyoyi masu tushe sun tabbatar wa Aminiya cewa ’yan ta’adda ne suka kai harin.
– Harin Boko Haram ne da Ansaru — Jami’an tsaro –
Wata babbar majiyar tsaro ta shaida wa wakilanmu cewa a ’yan kwanakin da suka wuce, jami’an tsaro sun kashe ’yan ta’adda da dama suna kokarin rusa gadojin da ke kan hanyar jirgin kasan tsakanin Abuja zuwa Kaduna.
“Akwai alamar hannun ISWAP da Ansaru a hare-haren nan, idan ka lura su ’yan bindiga so suke su sace mutane su samu kudi da su.
“Shi kuma wannan so ake kawai a hallaka mutanen cikin jirgin. Amma mun gode Allah ba su yi nasara ba,” inji majiyar.
Wata majiyar tsaro ta daban ma ta tabbatar mana cewa sun samu rahoton yukurin rusa daya daga cikin gadojin da ke kan hanyar jirgin kasar, amma jami’an tsaro suka matsa kaimi suka dakile hakan.
A lokacin da take gabatar da rahoton yanayin tsaronta, Gwamnatin Jihar Kaduna ta ce ta samu rahoto cewa ’yan ta’adda da ’yan bindiga na kara kulla dangantaka a jihar.
“Hukumomin tsaro na sane da tattaunawar da ake yi tsakanin ’yan ta’adda da ’yan bindiga. An kama ’yan Boko Haram da dama suna kokarin shigowa Jihar Kaduna.
“Kungiyar Ansaru kuma tana kara fito da kanta, kamar yadda aka ga ta yi wa mutum 21 yankan rago a yankin Inono na Karamar Hukumar Sabuwa ta Jihar Katsina,” kamar yadda Kwamishinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida na Jihar Kaduna, Samuel Aruwan, ya bayyana a jawabinsa.
– Ainihin abin ya faru — Ganau –
A ranar Laraba da dare ne dai aka fara samun bayani cewa fasinjojin jirgin kasan sun tsallake rijiya da baya daga harin ’yan ta’adda da ake zargi sun dasa nakiya, kuma wani jirgi dauke da fasinja daga Abuja zuwa Kaduna ya bi ta kan nakiyar.
Rahoton ya kara da cewa maharan sun bude wa jirgin wuta, da nufin hallaka direban, amma ya auna arziki.
Tsohon Shugaban Kungiyar ’Yan Jarida ta Najeriya reshen Jihar Kaduna, Garba Muhammad, na cikin fasinojin jirgin.
Ya ce, “Minti 40 kafin mu isa Kaduna, mun ji wani kara mai karfi, sai jami’an tsaro suka ce mu lafe. Daga nan su kuma suka rika kai-komo. Dole sai da muka bude tagogi saboda tsananin zafi; Daga wurin da jirgin ya tsaya mana iya hango babban titi.”
Da sanyin safiyar Alhamis kuma wasu maharan suka je suka kara lalata titin jirgin da nakiya, lamarin da ya da tilasta wa Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Kasa dakatar da zirga-zirgar jirage a daga Abuja zuwa Kaduna.
Fasinjojin jirgin sun ce jirgin da ya bar Abuja zuwa Kaduna ranar Laraba da Magariba ya taka nakiyar farko da aka dasa ne da masalin karfe 8 na dare.
Wakilin Aminiya da ke cikin jirgin ya ce sai da suka shafe awa shida da cikin daji bayan faruwar hakan kafin wani kan jirgi ta zo daga Rigasa ya ja jirgin da ya tsaya, suka isa Rigasar da misalin karfe 2.30 na dare.
Nakiya ta biyu kuma ta tashi ne a safiyar Alhamis bayan jirgin da ya taso daga Tashar Rigasa a Kaduna da misalin karfe 6.40 na safe ya bi ta kanta, lamarin da ya sa layin dogon lalacewa.
Tsohon dan Majalisar Dattawa mai wakiltar Kaduna Tsakiya, Sanata Shehu Sani, wanda fasinja ne a jirgin safen ya wallafa a shafinsa na Facebook.
“Yau (Alhamis) da safe ina hanyata ta tafiya a cikin jirgin kasa, jirign da muke ciki ya taka nakiya, wanda ya yi sanadiyyar lalacewar layin dogon.
“Saura kadan jirgin kasan ya sauka daga kan titinsa, Allah ne kawai Ya kiyaye,” inji Sanata Shehu Sani.
Shi kuma Abba Adamu Musa, fasinja a jirgin da ya baro Abuja karfe 7 na safe zuwa Kaduna a safiyar ya ce jirginsu ya tsaya ne karamar tashar jirgi da ke Jere.
“Mun shafe awa biyu a wuri daya, mun dauka injin jirgin ne ya samu matsala, sai daga baya muka fara ji cewa jirgin da ya taso daga Kaduna ya taka nakiya.
“Sai da aka yi dabara, jirgin ya wuce sannan ya ja namu muka koma Abuja tare,” inji shi.
– Masu abinci sun tsawalla farashi –
Wani fasinja a jirgin Labara, James Abraham, ya ce faruwar lamarin ke da wuya, masu sayar da abinci da cikin jirgin kasan suka tsawalla farashi.
“Abun mamaki shi ne ana cikin wannan tashin hankali sai mutanen na suka kara farashin abinci da abin sha a jirgin kasar. Ruwan sha ya kare, ga shi kishi ya dami mutane.
“Amma sai masu saya da abincin da ya kamata su taimaka wa mutane suka koma tatsar jama’a,” a cewarsa.
Don haka ya yi kira ga hukumar da ta gudanar da bincike kan abin da masu sayar da abinci a cikin jirign kasan suka yi.
– An dakatar da zirga-zirgar jirage –
A ranar Alhamis Hukumar Jiragen Kasa ta Najeriya ta sanar da dakatar da zirga-zigar jiragen kasa saboda abin da ta kaira ‘abin da a yi zato ba’.
“Wan abu ya fashe a titin jirgin kasan da ya shafi tankin jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna (AK10).”
Ta ce an kai jirgin dakin gyara domin tantance abin da ke damunsa sannan a yi gyara, amma ba a samu saarar rai ba.
Wakilinmu ya tattauna da Manajan Daraktan Hukumar, Fidet Okhiria, wanda a hirar da suka yi ta waya ya yi watsi da rahoton da ke cewa ’yan ta’adda ne suka kai wa jirgin hari.
Mista Okhiria ya ce sun fi zargin cewa barayin karafan titin jirgin kasa ne suka aikata, lura da karuwar sace-sacen karafan jirgin kasa da ake samu a baya bayan nan.
“Saboda wasu dalilai da suka sha karfinmu an dakatar da zirga-zirgar jiragen kasa nan take, domin kare lafiyar abokan huldarmu.
“Muna ci gaba da aiki domin daidaita komai, kuma nan gaba za mu sanar da ku da zarar an kammala gyare-gyare,” inji sanarwar.
Sai dai ba ta bayyana zuwa lokacin da ake sa ran dawowar zirga-zirgar jiragen ba kuma zuwa safiyar Alhamis dai ba a ci gaba da zirga-zirgar jirgi a wannan bangaren ba.
– Matafiya sun yi cirko-cirko –
Bayan lamarin da ya faru ranar Alhamis Aminiya ta ziyarci Tashar jirgin kasa da ke Rigasa a Kaduna inda ta iske daruruwan matafiya sun yi cirko-cirko.
Daga cikin matafiyan har da wani babban sarake da ayarinsa, wanda daga baya dole suka tafi.
Wata mata da ta bayyana sunanta a matsayin Hajiya, ta ce dole ita da mijinta suka koma gida saboda ba za su iya tafiya ta hanyar titi ba.
Shi kuma Abubakar Adam da ke hanyarsa ta zuwa Kaduna, ya ce, “Mun yi ta zama a cikin jirgi babu wanda zai iya mana bayani. Muna Kubwa lokacin da aka shaida mana cewa an samu jinkiri saboda jirgin ya samu matsala, haka muka yi ta jira na sama da awa daya, saboda haka aka yi ta zaton sai wanda ya taso daga Kaduna ya karaso.”
“Daga baya misalin karfe 12 na rana wasu jami’ai suka yi ta yawo, suka samo network sannan suka kira aka kawo mana dauki.”