✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Isra’ila za ta gina wa Yahudawa gidaje 3,144 a yankin Falasdinawa

Falasdinawa dai na kallon yunkurin a matsayin haramtacce.

Hukumomin kasar Isra’ila sun fara wani yunkuri na gina wa Yahudawa sabbin gidaje 3,144 a yankin gabar Yammacin Kogin Jordan da ta mamaye daga Falasdinawa.

Wani jami’i a Hukumar Tsaron Isra’ilan ya ce tuni kasar ta bayar da izinin fara sabbin gidaje kimanin 1,344, yayin da nan ba da jimawa ba za ta bayar da izinin karshe domin gina wasu guda 1,800, kamar yadda Kamfanin Dillancin Labarai na Reuters ya rawaito a ranar Alhamis.

Kazalika, wata kungiyar tabbatar da zaman lafiya mai zaman kanta ta kasar mai suna Peace Now ta tabbatar da yunkurin na Isra’ila.

Tuni dai Shugaban Falasdinawa Mahmud Abbas ya yi kira ga hukumomin kasa da kasa da su dauki tsattsauran matakin kan yunkurin na Isra’ila.

Ko da yake adadin gidajen da za a gina ba za su kai kwatankwacin wadanda aka gina zamanin mulkin Shugaban Amurka Donald Trump ba, sai dai ko da gida guda daya yana da tasiri a wajen Falasdinawa.

Wannan dai wani sabon yunkuri ne a fadi-tashin da Isra’ilan ke kokarin yi tsawon shekara 50 domin gine-gine Gabar Yammacin Kogin na Jordan da Yahudawa ’yan kama-wuri-zauna ke ci gaba da yi.

Dokokin kasa da kasa dai na kallon gidajen da Isra’ila take ginawa a yankunan da ta mamaye a matsayin haramtattu, sai dai gwamnatocin kasar daban-daban sun jima suna yin hakan, lamarin da ya jefa yarjejeniyar samar da kasashen Isra’ila da Falasdinu a matsayin makabtan juna cikin tsaka mai wuya.

Kakakin kungiyar Hamas ta Falasdinawa, Hazem Qassem, ya yi kira ga hukumomin kasar da ma na kasa da kasa da su taka wa Isra’ilan birki daga gine-ginen wadanda ya bayyana su a matsayin haramtattu.