✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Isra’ila ta tsagaita wuta a Lebanon

Yarjejeniyar tsagaita wutar ta soma aiki tun da Asubahin wannan Larabar.

Yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Isra’ila da ƙungiyar Hezbollah ta fara aiki da ƙarfe 4 na safiyar yau agogon ƙasar Lebanon, kuma kawo yanzu babu rahotanni saɓa yarjejeniyar da Amurka ta shiga tsakani a kowane ɓangare, matakin da tuni Iran ta yi maraba da shi.

Yarjejeniyar, wadda ta soma aiki da ƙarfe 4:00 na safe (0200 GMT), za ta sa Isra’ila ta daina yaƙin da take yi a Lebanon wanda ya kashe aƙalla mutum 4,000, da jikkata fiye da mutum 16,000 kana ya tilasta wa fiye da mutum miliyan ɗaya barin gidajensu.

Yarjejeniyar ta soma aiki awanni bayan Isra’ila ta ƙaddamar da mummunan luguden wuta ta sama a babban birnin ƙasar wato Beiruta wadda ke zuwa yayin da al’ummar yankin Gabas ta Tsakiya, waɗanda ke cikin mawuyacin hali, suke ɗari-ɗari game da ɗorewarta.

Mazauna Beirut sun riƙa bukukuwa na murnar aiwatar da wannan yarjejeniya kuma babu wasu rahotanni na ƙin yin biyayya ga yarjejeniyar tun da aka tsagaita wuta.

Yarjejeniyar tsagaita wutar wadda aka sanar da ita ranar Talata wani babban ci gaba ne wajen kawo ƙarshen yaƙin kusan watanni 14 da aka fafata baya ga ta’azzara yaƙin da Isra’ila take yi a Gaza.

A ɓangare guda, mayaƙan Hezbollah sun kashe sojojin Isra’ila aƙalla 82 da fararen-hula 47, a cewar hukumomi.

Isra’ila ta ce za ta kai hare-hare muddun ƙungiyar Hezbollah ta karya yarjejeniyar. Kawo yanzu Hezbollah ba ta ce komai ba game da lamarin.

Me yarjejeniyar ta ƙunsa?

A yammacin Talata ne Isra’ila da Faransa da Amurka suka sanar da ita, inda Shugaba Joe Biden ya ce ana fatan “za ta zama ta dindindin.”

Shugaban Amurka Joe Biden ya faɗa wa manema labarai cewa an tsara yarjejeniyar ce “da zimmar ta zama ta dindindin”.

A ƙarƙashin yarjejeniyar, cikin kwana 60 Hezbollah za ta janye dakarunta da makamai daga yankin da ake kira Blue Line — wata iyaka da ba ta hukuma ba tsakanin Isra’ila da Lebanon wadda aka ƙirƙira a ƙarshen yaƙin da suka gwabza a 2006 — da kuma kogin Litani da ke da nisan kilomita 30.

Dakarun sojin gwamnatin Lebanon za su maye gurbin mayaƙan Hezbollah a yankin, sannan su tabbatar babu wasu sauran makamai ko kayayyakin ƙungiyar da za a sake ginawa, a cewar wani babban jami’in Amurka.

Cikin wannan kwana 60 ɗin dai, Isra’ila za ta dinga janye dakaru da fararen hularta da suka rage, in ji Biden, yana mai cewa hakan zai bai wa fararen hula a ɓangarorin biyu damar komawa gidajensu.

“Wannan sanarwar za ta shimfiɗa ƙa’idojin samun zaman lafiya da zai bai wa ƴan ƙasashen biyu damar komawa gidajensu,” in ji wata sanarwar haɗin gwiwa da ta fito daga gwamnatocin Amurka da Faransa, ƙasashe biyu da za su taimaka wurin tabbatar da tsare-tsaren da ke ƙasa wanda za su aiwatar da ƙudurin Majalisar Dinkin Duniya da aka gabatar a ƙarshen yakin shekarar 2006.

Firaministan Lebanon, Najib Mikati ya yi maraba da yarjejeniyar, yana mai cewa wani muhimmin mataki ne na maido da zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasar tare da bai wa ƴan ƙasar damar komawa gida.

Sai dai kuma ya buƙaci Isra’ila ta “bi ƙa’idojin yarjejeniyar” ta fice daga yankunan da ta mamaye da kuma mutunta ƙudurin Majalisar Ɗinkin Duniya.

Shi kuwa Ministan Muhalli na ƙasar Labanon Nasser Yassin, ya shaida wa BBC cewa, ganin yadda ƙungiyar Hezbollah ta ci gaba da kasancewa a matsayin “jami’yya” a majalisar dokokin ƙasar, a yanzu ƙasarsa na buƙatar mayar da hankali kan maido da tsarin siyasa da sawwaƙa tattaunawa tsakanin “al’ummomi daban-daban”.