✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Isra’ila ta sake kakaba dokar kullen coronavirus

Kasar Isra’ila ta sake kakaba dokar kullen coronavirus a karo na biyu domin dakile ci gaba da yaduwarta, duk da zanga-zangar kin amincewa da ’yan…

Kasar Isra’ila ta sake kakaba dokar kullen coronavirus a karo na biyu domin dakile ci gaba da yaduwarta, duk da zanga-zangar kin amincewa da ’yan kasar su ka yi a kan matakin.

Akasarin ’yan kasar na yin boren ne saboda abin da suka kira mummunar illar da sake kulle kasar zai yi wa tattalin arzikinsu.

Kullen na tsawon mako uku ya fara ne sa’o’i kadan kafin sabuwar shekarar kasar da ake kira Rosh Hashana kuma zai shafi wasu bukukuwan addini kamar su Yom Kippur da ma na Sukkot.

Firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu ya ce, “Gwamnatinmu ba ta da wani zabi face sake sanya dokar saboda barazanar da muka hango na tunkararo mu.

“Sai da muka yi duba na tsanaki tsakanin lafiya da kuma kalubalen tattalin arziki kafin daukar wannan matakin”, inji Mista Netanyahu a yayin wani jawabi ga ’yan kasar ta talbijin a ranar Alhamis.”

Yawancin ’yan kasar dai na ci gaba da Allah-wadai da matakin da gwamnatin ta dauka.

Erez Berenbaum, daraktan wani asibiti da ke birnin Ashdod na kasar ya yi gargadin cewa rashin yin cikakken bayani daga bangaren gwamnatin na iya sa jama’a da dama su yi kunnen uwar-shegu da dokar.

To sai dai sabuwar dokar ta kebance wadanda za su fita waje domin sayen magunguna, abinci, halartar jana’iza da wasu muhimman bukatu.

Cutar COVID-19 dai ta kashe mutane 1,169 daga cikin mutane miliyan tara da ke kasar.