Isra’ila ta yi ikirarin kakaba wa kasar Iran takunkumin diflomasiyya da zai sa kasashe su yanke duk wata alaka da ita.
Ministan harkokin wajen Isra’ila, Katz, ya sanar da aika wa wadansu kasashen duniya bukatar su ma su yanke duk wata alaka da Iran.
Ya sa sanar a shafinsa na X cewa, “A safiyar Yau (Litinin) na aika wasiku zuwa kasashe 32, na kuma yi magana da ministocin harkokin waje da dama da kuma manyan mutane a kasashen duniya.”
Ministan harkokin wajen Isra’ilan ya yi kira da a sanya wa kasar Iran takunkumi, a kuma hana ta ci gaba da shirinta na Nukiliya.
- Jiragen Soji Sun Kashe Kwamandojin ISWAP A Borno
- Amurka ta gargadi Isra’ila kan shirin kai wa Iran hari
Hakazalika, Katz ya bukaci kasashen da ya aike wa wasika su ayyana Rundunar Sojin Mayakan Juyin Juya Halin Iran (IRGC) a matsayin kungiyar ta’addanci.
Katz ya yi imanin cewa, wadannan matakai in suka tabbata za su taimaka wurin rage wa kasar Iran karsashi.
Ya ce “Dole ne a dakatar da Iran daukar duk wani mataki na soji kafin lokaci ya kure.”
Katz ya bayyana cewa, akwai bukatar daukar wannan mataki a lokaci guda tare da yin amfani da karfin soji wurin tabbatar da zaman takunkumin ga Iran.
Ya ce, Iran fa ta yi amfani da muggan makamai masu linzami da jirage marasa matuki har guda 300 ga kasarsu.
Rundunar sojin Isra’ila ta bayyana cewa, ba ta da niyyar barin harin da Iran ta kai a daren Asabar ya wuce ba tare da ta mayar da martani ba.
Iran ta bayyana harin da ta kai a matsayin ramuwa, domin Isra’ila ta kai hari kan wani ofishin diflomasiyyarta a Siriya wanda ya yi sanadin mutuwar wasu janar-janar na Iran biyu da jami’ai biyar.
Kamar yadda Kamfanin Dillacin Labaran Najeriya ya ruwaito.