Mutane da dama ne ake fargabar sun mutu a wani hari da Isra’ila ta kai makarantar Al Fakhoura wadda ke dauke da dubban ‘yan gudun hijira a sansanin Jabalia da ke Arewacin Gaza.
Kungiyar Hamas ta ce wasu kazaman hare haren da Isra’ilan ta kai sansanin ‘yan gudun hijirar sun yi sanadiyar hallaka mutane sama da 80 a yau Asabar.
- NSCDC ta tura jami’ai iyakar Nijeriya da Nijar
- Mutumin da ya ’mutu’ ya dawo bayan shekaru 8 ya ci gaba da taimakon Hamas
Ma’aikatar harkokin wajen Falasdinu a wata sanarwa da ta fitar ta ce wannan ‘kisan kiyashin’ alama ce da ke nuna cewa yakin Isra’ila na son yi wa Arewacin Gaza karkaf.
Mai magana da yawun ma’aikatar lafiya ya ce akalla mutane 50 suka mutu sakamakon harin da Isra’ila ta kai yau da Asuba a makarantar Al-Fakhoura da ke cikin sansanin wanda ke karkashin Majalisar Dinkin Duniya, abinda ya haifar da suka daga kwamishinan jinkai na Majalisar.
Jami’an Majalisar dinkin duniya sun ce dubban mutanen da suka rasa matsugunansu ne suka samu mafaka a cikin makarantar da Isra’ila ta kai harin, abinda ya sa shugaban jinkai na Majalisar Martin Griffiths ya yi Allah wadai da harin, wanda ya ce ya ritsa da mata da yara da kuma maza.
Griffiths ya ce sansanin mastuguni ne na samun mafaka, yayin da kuma makarantar wuri ne na samun ilimi, saboda haka babu dalilin da zai sa a kai wa fararen hula hari, musamman wadanda suka samu mafaka.
Kamfanin Dillancin Labaran Faransa na AFP ya bayyana cewar hotunan wadanda harin ya ritsa da su sun mamaye kafofin sada zumunta, cikin su harda wadanda ke kwance a kasa jina-jina, duk da yake bai iya tantance sahihancinsu ba.
Sansanin ‘yan gudun hijirar Jabalia ne mafi girma a Arewacin Gaza, wanda ke dauke da Falasdinawa sama da miliyan guda da rabi wadanda yakin da ya barke na makwanni 6 ya raba da muhallansu.
Wasu kasashen Turai sun haramta gangamin goyon bayan Falasdinawa
Wasu daga cikin Turawan da ke son daga muryarsu domin nuna goyon baya ga Falasdinawa na fuskantar kalubale a kasashen da suke sakamakon haramcin da aka saka kan goyon bayan Falasdinawa da daga tutocinsu.
Tuni Birtaniya da Faransa da Switzerland da Jamus da Jamhuriyar Czech da Austria suka saka irin wannan takunkumin mai tsauri kan jama’ar da ke son fitowa fili don yin Allah wadai da kisan da Isra’ila ke ci gaba da yi a Gaza.
Kungiyoyi masu zaman kansu da dama daga ciki har da Amnesty International duk sun caccaki irin dabi’ar da kasashen suka nuna duk da ‘yancin tofa albarkacin baki da ke da akwai a kasashen.