✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Isra’ila ta hallaka jagoran Hezbollah Hassan Nasrallah

Wata majiya ta ce an kasa ji daga gare shi tun ranar Juma’a da daddare.

Isra’ila ta sanar da hallaka jagoran Hezbollah da ke samun goyon bayan Iran, Hassan Nasrallah tare da wasu kwamandojin kungiyar a kudancin Beirut.

Sai dai kawo yanzu Hezbollah ba ta fitar da sanarwa a hukumance ba.

Tun da farko, Isra’ila ta ce ta kai hari a hedkwatar ƙungiyar da kuma wuraren ajiye makamanta a babban birnin Lebanon, sannan kafofin watsa labaran Isra’ila da Amurka sun ruwaito cewa an kai harin na ranar Juma’a da daddare ne da zummar kashe Nasrallah.

Sai dai wata majiya ta kusa da Hezbollah ta ce “babu abin da ya samu” Nasrallah yana cikin “ƙoshin lafiya,” yayin da wata majiyar ta daban ta ce an kasa ji daga gare shi tun ranar Juma’a da daddare.

Isra’ila ta ƙaddamar da jerin zafafan hare-hare a kudancin Beirut ranar Juma’a da daddare wanda shi ne mafi girma da ta kai a yankin da Hezbollah ta fi ƙarfi tun yaƙin da suka yi a shekarar 2006.

Hayaki dai ya turnuku sararin samaniyar Beirut, tituna sun kasance fayau, kantuna a rufe ba ka jin motsin mutane.

Wata majiyar kamfanin dillancin labarai na Reuters ta shaida jin karar tashin makamai masu linzami sama da 20 ta sararin samaniya.

Dubban mutane sun kauracewa gidajensu a yankin na kudancin Beirut, inda suka nemi mafaka a gabar teku da dandanlin shahidai da kuma wasu wuraren na daban da ke kasancewa tudun mun tsira.