✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Isra’ila ta amince da tsagaita wuta na awa 4 kullum a Gaza

Ta ce tsagaita wutar domin a samu damar shigar da kayan tallafi

Kasar Isra’ila ta amince ta riƙa tsagaita wuta da kai hare-hare na awa hudu kullum a Zirin Gaza domin bayar da dama a shigar da kayan tallafi.

Kakakin Majalisar Tsaron kasar, John Kirby ne ya sanar da hakan da safiyar Alhamis.

John ya kuma shaida wa ’yan jarida cewa za a fara aiwatar da shirin tsagaita wutar ne daga yammacin Alhamis a Arewacin Zirin na Gaza.

Isra’ila dai ta shaida wa Amurka cewa za a sanar da lokutan tsagaita wutar sa’o’i uku kafin ya zo.

Shi ma wani jami’in gwamnatin ta Isra’ila ya cewa za a yi sassaucin ne domin a ba mutane tsallakawa Kudancin Zirin domin samun abinci da magunguna.

Shi ma Firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu, ya ce akwai yiwuwar su bude kofar sassautawa saboda dalilan shigar da kayan agaji, amma ba za su yarda da duk wani mataki na tsagaita wuta ba.