✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Israi’la ta aikata ‘laifukan yaki’ a Gaza

A shekaranjiya Laraba ne kungiyar kare hakkin dan Adam ta Amnesty International ta ce akwai ‘’kwakkwarar shaida’’ da ke cewa kasar Isra’ila ta aikata laifukan…

A shekaranjiya Laraba ne kungiyar kare hakkin dan Adam ta Amnesty International ta ce akwai ‘’kwakkwarar shaida’’ da ke cewa kasar Isra’ila ta aikata laifukan yaki yayin da take mai da martani kan cafke daya daga cikin jami’anta lokacin wani tashin hankali a yankin zirin Gaza.

kungiyar ta ce lugudan wutar da aka shafe kwanaki uku ana yi kan yankuna mai tarin jama’a, ya hallaka Palasdinawa a kalla 135. Sojojin Isra’ilar sun kaddamar da abin da rahoton na Amnesty International ya kira gagarumin hari a Gaza .
Sai dai Isra’ilar ta yi watsi da rahoton da cewa ya baiwa bangare daya fifiko.
An shafe kwanaki 50 a tashin hankalin tsakanin watan Yulin bara zuwa Agusta kafin a tsagaita wuta.