✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

‘Isra’ila na tsare da Falasdinawa kusan 600’

Kungiyar ta ce akasarin mutanen ana tsare da su ne ba tare da sun aikata wani laifi ba

Wata kungiya mai rajin kare hakkin dan Adam ta ce akalla mutum 600 ne hukumomin Isra’ila suka daure ba tare da aikata wani laifi ba.

Kungiyar mai suna HaMoked a ranar Litinin ta ce akalla fursunoni 604 ne ke tsare wanda mafi yawansu Falasdinawa ne.

Wannan, a cewar kungiyar shi ne adadi mafi yawan da aka samu tun shekarar 2016.

Kungiyar ta ce mafi yawan wadanda ke tsaren ba su san ma laifin da suka aikata ba kuma ba a ba su damar kare kansu ba a gaban kotu.

Har ila yau, ta ce fursunonin ana daure su ne har na tsawon wata shida kuma kara wasu watannin shida gabanin gama shari’ar da ake musu, wanda hakan kan haifar da zamansu a daure har na tsawon shekaru.

Sai dai a bangare guda kuma, hukumomin Isra’ilan sun ce wannan ita ce hanyar da suke bi domin tattara bayanai akan wandanda ake zargin, inda a gefe guda kuma kungiyar take sukar wannan tsarin hukumomin.

Har zuwa yanzu dai hukumar tsaron kasar Isra’ila ba ta ce komai ba akan wannan ikirarin da kingiyar ta yi.